✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Rubutun Hausa

Gasa a kowane fanni ne aka yi tana bayyanawa ko bankado mutane masu hazaka, basira, da hikima wadanda ba a san su ba. Na yi…

Gasa a kowane fanni ne aka yi tana bayyanawa ko bankado mutane masu hazaka, basira, da hikima wadanda ba a san su ba. Na yi dubi ga bangaren rubuce-rubuce. Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya a littafinsa mai suna, Hausa a Rubuce, Tarihin Rubuce-rubuce Cikin Hausa wanda ya rubuta a 1988, ya tabbatar da cewa, a 1933 ne aka bankado marubuta wadanda ba a mantawa da rubuce-rubucensu a kasar Hausa, wadanda sai a sakamakon gasar ta 1933 din ne, aka gano su. Marubutan su ne, Dokta Abubakar Imam da Malam  Bello Kagara da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Alhaji Muhammadu Gwarzo da Mista  John Tafida da sauransu.

Haka kuma, a gasar aka samu fitattun litattafan Hausa irin su Ruwan Bagaja (1935) na Abubakar Imam da Gandoki (1935) na Bello Kagara da Shaihu Umar (1935) na Abubakar Tafawa Balewa (1935), Jiki Magayi (1935) na John Tafida. Akwai litattafai da dama wadanda ake ganin cewa watakila da ba a sa gasar ba da wahala a same su. Shugaban da ya kafa gasar R.M East ya sha wahala, domin sai da ya rika bin mutane yana jan hankalinsu tare da nuna musu irin labarin da za a kago. Ko a yanzu da za a rika sa gasa tabbas da an bankado hazikan marubuta.

Nasiru Kainuwa Hadeja

08100229688