✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar zakarun kulob-kulob na Turai: Arsenal ta nuna da gaske take

Ga dukkan alamu kakar wasa ta bana za ta yi wa kulob din Arsenal da ke Ingila kyau ganin yadda kulob din yake haskakawa a…

Mesut Ozil (a tsakiya) tare da takwarorinsa ‘yan kwallon Arsenal a lokacin da yake murnar zura kwallo a ragar kulob din Napoli a ranar Talatar da ta wuceGa dukkan alamu kakar wasa ta bana za ta yi wa kulob din Arsenal da ke Ingila kyau ganin yadda kulob din yake haskakawa a gasar zakarun kulob-kulob a Nahiyar Tura (Champions League).
Ya zuwa ranar Talatar da ta wuce kulob din ya lashe wasanni biyu da ya buga a gasar da hakan ta sa yake saman tebur a jerin kungiyoyin da suke fafatawa a gasar a rukunin F.
Yanzu haka kulob din ya hada maki shida daga wasanni biyu da ya yi.
Shahararren dan kwallon Real Madrid a da, Mesut Ozil wanda ya canza sheka a ranar da aka rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo yana daga cikin ‘yan kwallon da suke taimakawa kulob din wajen samun nasara a wannan lokaci.
Hasalima, masana harkar kwallo sun tabbatar dan kwallon ne ya ba takwarorinsa ’yan wasan kulob din Arsenal kwarin gwiwar lashe wasanni a kan kari tun bayan da ya fara yi wa kulob din wasa a kakar wasa ta bana.
Masana harkar kwallo sun ce ba karamin kuskure kulob din Madrid da ke Sifen ya yi ba na sayar da Mesut Ozil ga Arsenal a kakar wasa ta bana ba, ganin yadda dan kwallo ne da ke da hazaka da kuma iya taka leda a duk lokacin da yake wasa.
Masana sun yi hasashen muddin kulob din na Arsenal ya cigaba da nuna kwazo kamar yadda yake yi a halin yanzu a gasar, babu shakka zai iya lashe kofin a karon farko tun bayan da kulob din ya taba kai wa ga wasan karshe a shekaru da dama da suka gabata.
Haka abin yake a gasar rukuni-rukuni na Ingila, inda kulob din Arsenal a yanzu haka yake saman tebur da yawan maki 15.
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa na kulob din sun yi hasashen muddin kulob din ya cigaba da nuna kwazo a gasar, babu shakka zai iya lashe kofin Premier a wannan karo.
Kimanin shekara takwas kenan rabon da kulob din Arsenal ya lashe kofi sai dai akwai yiwuwar ta sake zane a wannan karon ganin yadda kulob din yake haskakawa a wasannin da yake fafatawa.