Aminiya

Gasar Zakarun Turai: Madrid da Liberpool da Chelsea sun fara wasa da kafar hagu

A ranar Talatar da ta wuce  a fafatawar da aka yi a gasar cin Kofin Zakarun Turai, kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta sha kashi a hannun kungiyar Napoli ta Italiya da ci 2-0.

Wannan shi ne karo na farko tun  1994 da ake lallasa mai rike da kofin a wasan farko na gasar.  A wancan lokaci  an doke Kungiyar AC Milan ta Italiya  mai rike da kofin a wasanta na farko sai kuma wannan da ya faru ga Liberpool na Ingila.

ADVERTISEMENT

Haka kuma a wasan da Chelsea ta karbi bakuncin kulob din Balencia ta Spain, Balencia ce ta lallasa Chelsea da ci  daya mai ban haushi.

Sannan a shekaranjiya Laraba kulob din Paris Saint Germain (PSG) ya lallasa na Real Madrid da ci 3-0.  Magoya bayan kungiyoyin Liberpool da Madrid da Chelsea ba su ji dadin sakamakon wasannin ba kamar yadda rahotanni suka nuna.

ADVERTISEMENT