✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai: Yadda zagaye na biyu ke gudana

A wannan makon ne aka ci gaba da zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, inda aka fara kece-raini a tsakanin kungiyoyin da suka tsallaka zuwa…

A wannan makon ne aka ci gaba da zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, inda aka fara kece-raini a tsakanin kungiyoyin da suka tsallaka zuwa zagayen.

A ranar farko, wato ranar Talata, kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain (PSG) ce ta bi Manchester United har gida ta doke ta da ci 2 -0  a filin wasa na Old Trafford.

Presnel Kimpembe ne ya fara zura kwallo a minti na 53, sannan Kyalian Mpape ya zura kwallo ta biyu bayan minti bakwai.

Al’amarin Manchester United ya kara tabarbarewa a minti na 89, inda aka nuna wa Paul Pogba jan kati bayan ya kada Daniel Albes a kasa.

A wasan Manchester United ta kai hari sau 10, yayin da PSG ta kai hari 12. A cikin harin kuma na PSG biyar ne suka yi kusan shiga zare, yayin da ita kuma Man U sau daya kawai ta kai hari kusa da zare.

A takaice dai, za a iya cewa an yi wa Manchester United kaka-gida, inda aka zo har gida aka buge ta, sannan aka hana ta kuka, kamar wadansu suke cewa.

Kafin wannan wasan mai rikon kwaryar horar da ’yan wasan Manchester United Solskjaer ya samu nasarar lashe wasa 10 da yin kunnen doki  daya cikin wasanni 11 da suka fafata tun lokacin da aka nada shi kocin riko.

Manchester United za ta ziyarci gidan Paris St Germain a wasa na biyu zagaye na biyu na gasar a ranar 6 ga Maris, inda suke neman alkalla kwallo 3 idan suna son su fitar da kungiyar PSG, lamarin da yake da kamar wuya.

A wani bangaren kuma, Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, (UEFA) ta tuhumi Manchester United da PSG, bayan kammala wasan saboda yadda aka rika samun hargitsi a wasan musamman daga wajen magoya bayan kungiyoyin biyu.

UEFA ta tuhumi United da laifin magoya bayanta sun jefa abubuwa cikin fili, ita kuwa PSG ana tuhumar magoya bayanta da jefa abubuwa cikin fili da kunna wuta mai tartsatsi da lalata wasu abubuwa.

Magoya bayan Man United sun jefi tsohon dan wasansu wanda yake kungiyar PSG a yanzu wato Angel Di Maria da kwalba, inda aka nuno shi ya dauki kwalbar ya kai bakinsa, sannan daga baya ya jefar da ita kuma sun rika yi masa ihu idan ya dauki kwallo. Dan wasan ya rufe musu baki, domin ya nuna kwazo da kwarewa saboda shi ne ya taimaka wajen zura kwallaye biyu da PSG din ta ci.

Bayar fitar da tuhumar da aka yi kungiyoyin biyu, Hukumar EUFA ta fitar da ranar 28 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da kwamitin da’a na hukumar zai zauna don sauraren tuhumar don yanke hukunci.

A daya wasan kuma, Kungiyar A S Roma ta Italiya ce ta lallasa FC Porto ta kasar Portugal da ci 2 da 1 a gidan Roma.

Dan wasan Roma Nicolo Zaniolo ne ya zura kwallo biyu a ragar Porto a minti na 70 da kuma 76, sannan bayan minti biyu Adrian Lopez dan wasan Porto ya farke kwallo daya. A wasan dai za a iya cewa Roma ba ta da sa’a ce, domin ta kai munanan hare-hare guda 9.

A shekaranjiya Laraba kuma, Kungiyar Real Madrida mai rike da kofin ce ta tsira da kyar bayan ta kwaci kanta a hannun kungiyar Ajad ta kasar Holland. Kungiyar Ajad din dai ta yi rashin nasara ne a hannun Real Madrid da ci 2-1 a wasansu na farko zagaye na biyu.

Karim Benzema ne ya fara zura kwallo a ragar Ajad, sannan Ajad ta farke bayan minti 15, inda Hakim Ziyech ya zura kwallon a ragar Real Madrid.

Bayan an ci gaba da fafatawa a tsakanin kungiyoyin na tsawon lokaci, saura minti uku a tashi dan wasan Real Madrid Marco Asensio da ya shigo bayan hutun rabin lokaci ya zura kwallo ta biyu a ragar Ajad.

Sai dai masu sharhi suna ganin kawai Real Madrid ta samu sa’a a kan Ajad din ba wai ta fi cancanta ta lashe wasar ba ne domin kuwa Ajad ta taka leda iya takawa, kuma dan wasanta Nicolas Tagliafico ya zura kwallo, amma alkalin wasa ya soke bayan da ya kalli bidiyon da ke taimaka wa alkalan wasan wajen ganin abin da ya shige musu duhu wanda ke taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci.

A tarihi dai Real Madrid ta lashe kofin sau 13, yayin da ita kuma Ajad ta ci sau hudu.

Ajad za ta ziyarci Madrid a wasa na biyu a ranar 5 ga watan Maris.

A dayan wasan kuma na shekaranjiya Laraba, kungiyar Tottenham ce ta lallasa Dortmund da ci 3-0, a wani wasa da za a iya cewa mafi sauki a wannan mako.