✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gayyatar Rahama Sadau muka yi —’Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta gayyaci Rahama Sadau zuwa ofishinta ne amma ba tsare jarumar ta yi  ba…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta gayyaci Rahama Sadau zuwa ofishinta ne amma ba tsare jarumar ta yi  ba kamar yadda ake rade-radi.

Majiyar ’yan sanda a jihar ta shaida wa Aminiya cewa Shugaban ’Yan Sandan NajerriyaMohammed Adamu ne ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya gudanar da bincike kan rudanin da hotunan da jarumar ta masana’antar fina-finai ta Kannywood ta wallafa, wanda ya kai ga wani mutum daga cikin masu sharhi a kan hotunan ya yi batanci ga Manzon Allah S.A.W.

Majiyar ta kara da cewa Rahama Sadau ta koma Abuja tare don gudun kada a farmake ta a Kaduna, kafin daga bisani hukumar ’yan sandan ta gayyace ta zuwa Kaduna domin amsa tambayoyi.

Gayyatar na zuwa ne bayan wani mai suna Mallam Lawal Mohammed Gusau ya shigar da korafi a kan jarumar a ranar 3 ga watan Oktoba 2020, dangane da batancin da hotunan da ta wallafa suka jawo wa Manzon Allah (SAW).

Kafin shigar da kara a kanta, Rahama Sadau ta bayyana a wani bidiyo a yanayi na ban tausayi da nadama, inda ta nemi afuwar dukkanin Musulmi game da lamarin.

Har wa yau, a yayin hirarta da sashen Hausa na BBC, jarumar ta bayyana cewa ya kamata jama’a su tausaya mata domin ta fi kowa shiga damuwa a kan lamarin.