✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gazawar Gwamna Matawalle ta fara bayyana a Zamfara – Yari

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’azizi Yari Abubakar ya maida martani game da zargin haddasa tashin hankali da Gwamna mai ci a jihar Alhaji Bello…

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’azizi Yari Abubakar ya maida martani game da zargin haddasa tashin hankali da Gwamna mai ci a jihar Alhaji Bello Matawalle ya yi masa.

Martanin ya fito ne daga bakin Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, wanda daya ne daga cikin mamboban kwamitin hulda da ’yan jarida na Jami’iyyar APC a Jihar Zamfara.

A taron manema labarai, Alhaji Ibrahim Danmaliki ya bayyana zarge-zargen da Gwamnan ya yi a hirarsa da sashin Hausa na BBC a matsayin marasa tushe, kuma a cewarsa Gwamnan kame-kame yake yi saboda gazawa.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya zargi tsohon Gwamnan da hada baki da ’yan ta’adda don yi wa shirin zaman lafiyar da ya samar zagon kasa.

Tuni dai bangaren tsohon Gwamnan ya kalubalanci Gwamna Matawalle ya fadi daya daga cikin hare-haren da aka kitsa a lokacin da Abdul’aziz Yari ke cikin jihar.

Kwamitin ya ce tsohon Gwamnan bai taba zuwa wata karamar hukuma b, a jihar in ban da mahaifarsa Talata Mafara tun bayan saukarsa daga mulki.

Haka ya ce rashin amsa gayyatar da kwamitin bincike kan matsalar tsaro ya yi wa tsohon Gwamnan na da nasaba da jan kunnen da Gwamna Matawalle ya yi masa na ya cire hannunsa kan duk wani abu da ya shafi tsaro a jihar.