✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Genoa ta karya kwarin Jubentus a gasar Seria A

A makon jiya ne kungiyar Genoa ta yi nasarar doke Jubentus da ci 2-0 a wasan mako na 28 a gasar cin Kofin Serie A,…

A makon jiya ne kungiyar Genoa ta yi nasarar doke Jubentus da ci 2-0 a wasan mako na 28 a gasar cin Kofin Serie A, wanda shi ne karo na farko da aka doke kungiyar a kakar bana.

Genoa ta ci kwallon farko ta hannun Stefano Sturaro, sannan ta kara ta biyu saura minti tara a tashi wasa ta hannun Goran Pandeb.

Cristiano Ronaldo wanda ya ci wa Jubentus kwallo uku rigis a gasar cin Kofin Zakarun Turai da ta doke Atletico Madrid a tsakiyar mako, bai buga wasan ba inda wadansu suke ganin ya taimaka wajen rashin samun nasarar kungiyar.

Kungiyar Jubentus ta buga tare da doke dukan manyan kungiyoyin kasar, amma sai kungiyar Genoa ta karya mata kwari ta doke ta a wasansu karo na biyu, kamar yadda Jubentus din ta sha da kyar a hannunta a wasa na farko

Duk da haka Jubentus ce ta daya a kan teburin gasar, kuma ta bai wa Napoli wadda ita ce ta biyu tazarar maki 18.