✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ghana da Najeriya: Allah daya gari bamban (2)

Kamar yadda na ambata, dan siyasar da ya bar gadon mulki, alhali bai tara makudan kudi isassu ba, cikin lokaci zai tsiyace, musamman idan ya…

Kamar yadda na ambata, dan siyasar da ya bar gadon mulki, alhali bai tara makudan kudi isassu ba, cikin lokaci zai tsiyace, musamman idan ya zabi ya zauna Abuja. Misali a ce ya mallaki Naira miliyan 160, bari mu kididdiga abin da wannan adadin zai saya, a Abuja.
Idan a ce ministan ya aje aiki kuma ya mallaki ’yan miliyoyin daloli kuma ya ce zai yi rayuwar matsakaitan mutane a Abuja, sannan kuma bai mallaki gidan kansa ba, to ya sani, jimillar kudin nan da ya mallaka, gida daya kacal za su saya masa a Wuse II, kuma ba zai samu rarar da zai kayata shi da kayan kwalliyar ba, kamar gadaje da kujeru da tebura da sauransu. Gidan fa kuma ba gingimeme ba, domin kuwa gidan zamani a Asokoro ko Maitama, sai ya ka tanadi Naira biliyan daya kafin ka mallake shi, ko ma fiye da haka. Don haka ministan da ya mallaki tsirarun kudi, ba zai ma iya mallakar gida a irin wadannan unguwanni ba na Abuja.
Mu dauki ma cewa ministan nan ya mallaki gidan kansa da tawagar motocin shiga na alfarma kafin ya aje aiki, to ya sani cewa akwai bukatar kudin da zai rika zuba masu mai da na kula da su, akwai bukatar kudin biyan hadiman gida, akwai kudin sayen man dizal domin janareto. Haka kuma akwai kudin biyan makarantar yara, makarantun da ke da dan karen tsada. Akwai bukatar kudin asibiti domin kula da lafiya – asibitocin kudi a Abuja kuwa shegen tsada ke da su. Ba nan batun ya tsaya ba, dole ne ministan ya tanadi kudin da zai rika tallafa wa ’yan uwa da abokan arziki da suke karkara da tsofaffin abokan da suka yi makaranta tare a can baya. Akwai kuma batun neman taimako daga masallatai da majami’u. Adadin kudin da mutum zai kashe a wata daya a irin wannan hidima, za su kai miliyoyin Naira. Idan a ce ba makudan kudi ya tara ba, to kuwa cikin shekara daya ko kasa da haka, zai iya talaucewa.
Wani abu da ya kamata mu sani shi ne, babban dan siyasa a Najeriya, bai kamata ya mallaki gida daya ba kacal. Idan yana da gida daya a Abuja, to kuma akwai bukatar ya mallaki wasu a garinsa na haihuwa, kamar kuma yadda zai mallaki wasu a babban birnin jiharsu. Idan har irin wannan dan siyasa bai mallaki gida a garinsu ko a babban birnin jiharsu ba, to kuwa ya jaza wa kansa hanyar suka da zagi daga abokan adawarsa, su rika cewa shi mai kyamar mutanen garinsu ne. Haka kuma, za su rika cewa bai damu da karamar hukumarsu ba da sauran al’ummar yankinsu. Don haka, ya zama wajibi ga tsohon minista ya saba da kai gudunmowa ga al’ummar yankinsu.
Baya ga wannan, idan Musulmi ne shi ko Kirista, to ya dinga samun bukatun neman taimako ke nan daga masallacin da yake Sallah ko kuma cocin da yake zuwa bauta. Za su rika neman tallafin kudi doming gyare-gyaren masallacin ko cocin. Su ma ’yan banga na unguwa, za su matsa masa da neman tallafi, domin kuwa za su gaya masa cewa ’yan sanda ba za su iya ba da tsaro ga al’ummar yankin ba. Ya zama dole ya rika ba su tallafi, domin kuwa babu mamaki idan ya kiya, su kasance ma su ne za su dawo su yi masa fashi. Idan yana ba su tallafi kuwa, to kamar yana biyan haraji ne gare su, don kada su yi masa ta’adi.
Kuma duk da cewa kai tsohon minista ne, akwai bukatar ka rika zuwa kauyenku ko garinku lokaci-lokaci. Kan haka, duk lokacin da aka ga hanjin motocinka sun shigo gari, talakawa da suka dade cikin talauci, za ka ga sun yo tururuwa zuwa kofar gidanka, kuma kowa na tsammanin ka ba shi wani abu, saboda idan ba irinku na zuwa ba, sai ya dade bai kama Naira dari daya ba.
Irin wannan tsohon minista, muna la’akari da cewa ba zai shiga siyasa tsundun ba, zai hakura ya zauna a matsayinsa na tsohon ma’aikacin gwamnati. Sai dai irin wannan ba haka take kasancewa ba a mafi yawan lokaci. Irin wadannan mutane, za ka ga bayan sun aje aiki, sun kuma tsunduma cikin siyasa, ana ci gaba da damawa da su. Na taba tambayar wani mutum wanda tun a Jamhuriya ta farko yake siyasa, kuma har yanzu ana damawa da shi, cewa me ya sa har yanzu yake cikin siyasa. Shi ba wani babban dan siyasa ba ne kuma bai mallaki dogon ilimi ba, amma dai dan siyasa ne na tsaka-tsaki. Ya shaida mani cewa, shi a rayuwarsa, abin da ya tsana shi ne, ya wayi gari babu taron mutane a kofar gidansa.
A Najeriya, duk wanda ya taba dandana mulki, ba ya so ya bari, dalili ke nan za ka ga suna ta sarka-sarkar dawwama ko kuma idan mulkin ya kubuce, su yi ta kokarin dawowa. Da yawa za ka samu tsofaffin shugabannin kananan hukumomi suna kiciniyar zama ’yan majalisa, za ka ga tsofaffin ’yan majalisa suna kokarin zama ministoci, za ka ga tsofaffin ministoci suna kokarin zama gwamnoni; kamar kuma yadda za ka ga tsofaffin gwamnoni na kiciniyar zama shugaban kasa.
Ga dan siyasar da ya bar mulki kuma bai mallaki makudan kudi na fitar hankali ba, sannan kuma ya ce zai yi irin rayuwar da muka zayyana a sama, to lallai ya debo ruwan dafa kansa da kansa. Idan ’yan tsirarun miliyoyin Naira ya mallaka, cikin kankanen lokaci zai talauce. A Ghana fa, ga wata minista, kawai don ta yi burin mallakar Dala miliyan daya, an kore ta daga mulki. Lallai wannan shi ne ‘Allah daya gari bamban!’