✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ghana ta doke Najeriya a gasar  dafa shinkafa dafa-duka

A karon farko kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar a tsakanin Najeriya da Ghana a dandalin taro na Cressal…

A karon farko kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar a tsakanin Najeriya da Ghana a dandalin taro na Cressal Park da ke birnin Accra.

Wani rahoto da sashin Hausa na BBC ya wallafa a Intanet, ya bayyana yadda gasar ta kasance a tsakanin kasashen biyu wato Najeriya da Ghana. Da ma wannan batu ya jima yana jawo ce-ce kuce a shafukan sada zumunta kan wace kasa ce tafi iya girka shinkafa dafa-duka.

A wannan karo Kamfanin Kayayyakin girki na Onga ne ya raba gardama, yayin da ya shirya gasar domin zaben gwana a cikin kasashen biyu.

Madam Sika daga kasar Ghana ce  ta lashe gasar inda ta samu kyautar tsabar kudi har Dalar Amurka 2000 (kimanin Naira dubu 720).

Shinkafa dafa-duka nau’in abinci ne mai farin jini a kasashen Nahiyar Afirka da dama.

 ‘Yar Najeriya ce ta zo ta biyu a kasar, inda ta samu kyautar Dala 1000
‘Yar Najeriya ce ta zo ta biyu a kasar, inda ta samu kyautar Dala 1000

Akwai dadaddiyar hamayya ta raha a tsakanin Najeriya da Ghana a kan wace kasa ce a cikinsu dafa-dukarta ta fi dadi, musamman a kafafen sada zumunta.

Wadanda suka shirya gasar sun ce sun yi ne don kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu kuma suna fata gasar ta dore a gaba.