✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ghana za ta koro ‘yan matan  Najeriya

Hukumar Kula da Shigi da Fici ta kasar Ghana tana shirin dawo da wadansu mata ’yan Najeriya su 25, da ta kama suna karuwanci. Wani…

Hukumar Kula da Shigi da Fici ta kasar Ghana tana shirin dawo da wadansu mata ’yan Najeriya su 25, da ta kama suna karuwanci. Wani babban jami’in hukumar ya bayyana wa ’yan jarida haka a farkon wannan mako.

Enoch Annor Abrokwa na Hukumar Shigi da Ficen da ke kula da Shiyyar Bono ta Gabas, ya tabbatar da cewa za su dawo da ’yan Najeriya 25 da suka kama a Bono ba su da takardun shiga kasar. Ya kara da cewa da zarar an kammala shirye-shiryen da ake yi, za a tattara wadannan mata zuwa Najeriya inda su ka fito kamar yadda Aminiya ta samu labari.

An kama wadannan ’yan mata ne bayan wani umarni da Ministan Yankin Kasar, Kofi Amaokohere, ya bayar, inda ya nemi jami’an tsaro su hada dukkan masu laifin da suka tare a yankin. Jami’in ya shaida wa manema labarai cewa an kama karuwan ne a Kudancin garurwan Nkoranza da Kintampo lokacin da ma’aikata suke sinitirin dare.

A cewarsa “Ma’aikatanmu sun kutsa wasu hatsabiban lunguna ne da misalin karfe 12:00 zuwa 3:00 na dare, a wata rana inda muka kama wadansu karuwai 25, dukkansu ’yan Najeriya,” inji shi.

Babban Sufirintada Annor Abrokwa ya c: “Dukkan ’yan matan babu wata mai alamar shaida irin ta katin zabe, fasfo ko katin dan kasa.” Annor ya ce za a fara shirin maida su kasarsu.