✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidaje akalla 10 sun rufta a Onitsha

Gine-gine akalla 10 ne, ciki har da makaranta da majami’a, suka ruguje a karamar hukumar Onitsha ta Arewa da ke jihar Anambra sakamakon wata zaizayar…

Gine-gine akalla 10 ne, ciki har da makaranta da majami’a, suka ruguje a karamar hukumar Onitsha ta Arewa da ke jihar Anambra sakamakon wata zaizayar kasa da ruwan sama kama da bakin kwarya ya haddasa.

Wani mazaunin yankin, Godwin Aniakor, ya bayyana takaicinsa da dimbin dukiyar da ta salwanta.

Mista Aniakor ya ce mutane da dama sun rasa muhallansu, sannan ya yi bayanin cewa zaizayar kasar ta fara ne shekaru takwas da suka gabata.

Shi ma Christian Onwudinjo mazaunin yankin ne wanda, yayin da yake kwashe baraguzan gidanshi, ya ce tun da da ma suna rayuwa ne cikin hadari, sun fara shirin tashi daga wurin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa da ma dai al’ummar yankin da abin ya faru na fuskantar barazana daga zaizayar wadda ke hana su barci.

Ko a watan Oktoban bara ma Ministar Muhalli Sharon Ikeazor tare da Mataimakin Gwamna Nkem Okeke sun ziyarci wurin, inda suka yi alkawarin za a yi aiki don shawo kan matsalar.

Sai dai dan majalisar jiha mai wakiltar Mazaba ta 2 ta Onitsha ta Arewa, Edward Ibuzo, ya bayyana lamarin da cewa “yana bukatar kulawa ta gaggawa”.

Ibuzo, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Muhalli na Majalisar Dokokin Jihar Anambra, ya bayyana alhininsa da faruwar wannan lamari.

“An tattauna wannan batu a zauren majalisa kuma mun sanar da gwamnan jiha, har ma gwamnatin tarayya ta aiko da wata tawaga ta ga barnar da zaizayar ke yi.

“Ya kamata a rika daukar abubuwa irin wannan da muhimmanci saboda sun shafi rayuwa da dukiyar al’umma wadanda [kare su] alhaki ne na gwamnati”, inji Mista Ibuzo.