Da Dumi Dumi

Gidajen kangararru:  Abubuwan da suke faruwa da kuma samamen ’yan sanda

Amakonni uku da suka gabata ne ’yan sanda suka fara far wa makarantun allo ko gidajen kula da kangararru da masu tabin hankali suna sakin mutanen da suka iske daure a mari tare da tarwatsa makarantu ko cibiyoyin da kuma kama malamai da masu kula da su bisa zargin suna cin zarafin yara.                                                                                         Wakilanmu sun bibiyi al’amuran ganin yadda suke ci gaba da gudana a jihohin Arewa.                                                                                                                                                       Malam Lawan Yusuf Muduru, wanda aka fi sani da Malam Niga, yana daya daga cikin masu irin wadannan cibiyoyi inda yake da gidan horar da kangararrun a Unguwar Rigasa, Kaduna. Ya bayyana wa Aminiya cewa duk labarin da ake yadawa na cin zarafin yara da ake kai su gidan nasa, ba gaskiya ba ne. Ya cea babu wani koke da dalibai ko iyayensu ko al’ummar gari ke yi game da yadda suke kula da yaran.

“Kawai dai an yi min dirar mikiya ne saboda ayyukan da nake yi kuma bai kamata a ce an rufe wurin nan ko an kwashe daliban ba tare da wasu koke-koke ba. Daga baya-baya ne aka kirkiri koke-koken amma ni tsawon lokacin da na yi ina ayyuka ban san da wasu matsaloli ba. Bilhasali ma, tare da daliban nan a cikin gidan nan nake kwana, ban kuma san da wasu abubuwa da ake aikawata ba. Amma saboda mutum ya samu kubuta daga aikata ba daidai, dole su ce ana yin wadannan abubuwa. Idan ba haka ba, ai gwamnati ba za ta samu laifin da zai sa ta rike yaran ko ta sallame su ko a mika su ga iyayensu ba. Dole sai an samu ire-iren wadannan koke-koke. Idan kuwa suka ce alheri ake yi a wurin nan lallai za a yi kokarin dawo da su, domin ci gaba da zama har zuwa lokacin da iyayensu suka karbe su,” inji Malam Niga.

Game da ko yana ganin akwai siyasa a cikin wannan mataki tunda duk a Arewa ake yi, sai ya ce “Gaskiya akwai siyasa a cikin wannan lamari saboda duk inda aka je za a ce wai maza na bin maza ko mata na bin mata ko maza na bin mata, ko a ce akwai rashin tsabta da sauransu. Amma mu duk ba a same mu da wadannan abubuwa ba a cikin shekara 15, sai a kwana daya kawai za a ce an samu wannan? Na tabbata har ga Allah duk abubuwan da ake yi a wannan wuri ba boyayyu ba ne. Sannan muna da tsofaffin dalibai kusan 2,200, a je a tambaye su don samun tabbacin abin da ake yi a nan wurin ba wanda ke daure yana kokarin ta ina zai kubuta, sannan ga shi hankalinsu ba daidai ba, kuma a ce wai shi za a tambaya ya fadi abubuwan da ake yi a wannan wuri. Karya zai fadi ko sharri tunda yana son ya kubuta.”

“Ka ga ai sharruka za su yi domin su kubuta su koma gidajensu domin ci gaba da tsula tsiya, da su da wadanda ake tsoratar da su, cewa za a kawo su nan. Ka ga idan suna da tabbacin an rufe wuraren, babu wani wurin da za a yi musu barazanar za a kai su. Don haka sai su yi abin da suke so,” inji shi.

Game da ko ya hango za a iya samun barazanar tsaro a cikin al’umma dangane da matakin gwamnati na rufe irin wadannan gidaje, sai ya ce, “Babban tunanin da nake lallai badala za ta kara yawa, domin in ka duba da wannan makaranta da ta Daura da ta Katsina, a karanci ana rike da mutum kusan dubu biyu da ’yan kai. To, yanzu aka ce mutum dubu biyu sun watsu sannan akwai wadanda ake da niyyar kawowa ko ake musu barazanar za a kawo su, idan ba su daina abin da suke yi ba, kuma karshenta sun ninka wadannan, sai ya zama da wadannan da wadancan sun tabbata gwamnati ta rufe wuraren ba tare da ta gina nata ba, wanda za a iya kai su ba.

ADVERTISEMENT

“Ka ga misali nawa da aka kwashe su, da a ce an kai su inda gwamnati ta gina nata ne, da kila su kangararrun ba su yi sharrurrukan ba, saboda za su kubuta ne babu inda za a kai su, shi ya sa za su yi duk sharrin da suka ka ga dama domin kubutar da kansu. Ka ga ke nan da wadannan da wadancan za su hadu su rika tsula tsiyarsu a inda suke so kuma suka ga dama.

“Watakila wadansu su koma ’yan fashi wadansu kila masu garkuwa da mutane wadansu kuma barayi. Yanzu idan ka lura, saboda wayar hannu sai a kashe mutum. A wasu wuraren kuma ga ’yan-sara-suka da sauransu. Idan dnka ya addabe ka, idan akwai inda za ka kai shi ko ka yi masa barazana, sai ka samu kwanciyar hankali. ’Yan uwa da ’yan unguwa ma sai su samu kwanciyar hankali. Amma sai ya zamana yanzu an rufe wuraren nan, ka ga za a iya samun babbar barazana, wadda za ta tayar wa da kowa hankali,” inji shi.

Kwamishinar Kula da Al’umma da Walwalarsu ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta ce iyaye na da laifi sosai kan rashin kula da ’ya’yansu, wanda hakan ya sa suke kai su gidanjen horar da su. “Idan ba a Arewa ba, wa yake haifar yaro dan karami ya ce wai zai kai wajen horar da yara? Ai wannan yawanci sai a Arewa saboda kawai wadansu iyayen suna gudan daukar nauyin da Allah Ya dora musu na kula tare da bayar da tarbiyarsu,” inji ta.

A Jihar Bauchi kuwa, Aminiya ta gana da Shugaban Cibiyar Ladabtar da Kangararru da aka fi sani da Malam Kawu Rehabilitation Center, Alhaji Abdullahi Muhammad Tahir, inda ya ce su ba su da matsalar gana wa yara ukuba ko yin luwadi ko aikata ayyukan assha a cibiyarsu.

Malam Tahir ya ce sun bi dukkan ka’idojin da doka ta tanada kafin su kafa cibiyar kuma sun yi rajista da Karamar Hukumar Bauchi da Gwamnatin Jihar Bauchi, sun yi rajista da Gwamnatin Tarayya kuma suna da izinin gudanar da wannan cibiya, ba a Jihar Bauchi kawai ba, za su iya budewa a kowace jihar da ke Arewa.

Ya ce jami’an tsaro da Limamin Bauchi da kungiyoyin addinai daban-daban da hukumomin gwamnati suna ziyartar cibiyar kuma suna yaba irin kokarin da suke yi.

Malam Tahir ya ce “Cibiyarmu ta horar da kangararrun yara, ciki har da ’ya’yan manya kuma muhimman mutane a kasar nan da suka zauna a wajenmu tsawon wata shida kuma sun samu lafiya, dukkansu an sallame su sun koma gida.”

Ya ce suna da dokoki da suke taimakawa wajen tarbiyya a gida, don ba su bari mutum biyu su kwana a kan gado daya, kuma ba su barin mutum biyu su shiga bayan gida a lokaci guda.

“Hukumomin tsaro da kungiyoyi na ciki da waje babu wanda bai zo ya duba cibiyar ba. Hukumomin lafiya, ciki har da na duniya (WHO) sun zo sun ziyarci cibiyar, sun kuma dora mu a kan shawarwari kuma duk hukumar da ta ba mu shawara muna bi. Hukumomin kare hakkin dan Adam ma sun zo, sun duba  cibiyar. Don haka wannan cibiyar horar da kangararru ta sha bamban da wadanda ba su cika ka’ida ba,” inji Tahir.

Ya ce mari da sarka da ake kakaba wa kangararru da gagararru tilas take jawo haka. Ya ce mari wata dabara ce ta tsaro, domin kowace al’umma tana da dabarar yadda take tabbatar da tsaronta. “Idan aka ce za a rufe irin wadannan cibiyoyi, to lallai gwamnati ba ta da gidajen yarin da za ta iya ajiye marasa ji kuma wani dole sai an bi irin matakan da muke bi na addu’a da baiwa da Allah Ya yi mana kafin mutum ya gyaru. Don haka rufewar ba mafita ba ce, gwamnati ta daina biye wa jita-jita, ya kamata ta fuskaci matsalolin da suke fuskantar kasar nan,” inji shi.

Wani mai kula da makarantar tsangaya, Alaramma Salihu Musa ya ce “A makarantarmu muna karantar da yara kuma a kowace shekara suna haddace Alkur’ani. Kowane lokaci da wuya in ka san tarihin makarantun tsangaya ka ce ba a horar da dalibin da ke neman kangarewa. Amma cikin dalibai dubu da kyar ka samu uku saboda shi Alkur’ani kansa shiriya ne, ayoyin da ake karantar da dalibai suna shiryar da mutane ne.”

A Kano, Aminiya ta gana da Sheikh Manzo Arzai Shugaban Makarantar Alkur’ani ta Ma’ahad, wacce tsohuwar makaranata ce da ta shafe shekara 50 ana karatu tare da horar da kangararrun yara har ma da manya a cikinta. Sai dai a wannan lokaci makarantar ta rufe sashen horar da kangararrun, inda ta umarci dukkan iyayen yaran su je su dauki ’ya’yansu don kauce wa mamayar ’yan sandan.

 Wani vangare na Makarantar Arzai da ke Karamar Hukumar Dala, Kano
Wani vangare na Makarantar Arzai da ke Karamar Hukumar Dala, Kano

Sheikh Arzai ya shaida wa Aminiya cewa makarantarsu ta dauki matakin sallamar yaran da ke daure a mari su sama da 150 ne domin su tsira da mutuncinsu. “Tun daga lokacin da muka samu labarin yadda gwamnati ta shigo cikin lamarin da kuma yadda abubuwa suka faru a Kaduna da Katsina ya sa muka rufe wannan bangaren namu, saboda mu tsira da mutuncinmu. Mun buga wa iyayen yara waya suka zo suka dauki ’ya’yansu. A yanzu haka kin ga wurin ’yan kadan da suka rage ga su nan suna wanke kayansu za su tafi. Amma muna ci gaba da gudanar da sauran bangarorin bayar da ilimi a wannan makaranta kamar yadda muka saba,” inji shi.

Malam Habibu Arzai ya ce dama tun asali suna da tsarin yadda suke karbar yara a makarantarsu.  “Kasancewar ana kawo mana yara daga garuruwa ciki da wajen Najeriya, domin a nan babu jihar da ba a kawo mana yara a  Najeriya. Haka makwabtanmu irin su Kamaru da Nijar da Chadi da sauransu. Idan iyaye suka kawo mana yara za su cika fom na bayanan kansu da wurin da suke zaune da sauransu. Haka suna ajiye kudin abincin ’ya’yansu na watanni kafin su sake aiko da wani daga baya. Kowane uba yana hado dansa da kayan shimfidarsa da suka hada da tabarma ko katifa da bargo da sauransu da kayan amfani da suka hada da man shafawa da sabulun wanka da na wanki da sauransu. Mun tanadar musu da wurin kwanansu a kebance. Haka wurin da suke karatu daban yake. Muna ba iyaye dama su ziyarci ’ya’yansu don sanin halin da suke ciki,” inji shi.

Malamin ya ce “Hikimar sanya wa yara mari ita ce ba don azabtarwa ba ce, illa don a tsare su domin kada su gudu, saboda suna kan ganiyar aikata laifuffuka. Idan aka kawo mana yaro da farko za mu fara sa masa mari. Kuma ba mu ba yaranmu horo mai tsanani na duka ko wani abu makamancinsa, illa iyaka idan yaro ya yi laifi za a dake shi da bulala, dukan da za a iya yi wa kowane dalibin makaranta yayin da ya yi laifi.”

Game da zargin ana yin badala a irin wadannan gidaje na kangararru, Malam Habibu ya ce “Tun daga lokacin da na taso a wannan gida, sama da shekara 40 ban taba jin labari ko ganin an samu dalibanmu suna aikata ayyukan assha na neman maza a tsakaninsu ba. Ko kuma mu samu korafi daga iyaye cewa bayan yaransu sun koma gida suna nuna irin wannan hali a can ba.”

Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su duba a tsanaki a kan wannnan abu da ya taso, domin a nemo bakin zaren, ta yadda za a kawo gyara a cikin lamarin.

“Mun san cewa wake daya yana iya bata gari, kowace irin makaranta da tsarinta. Amma duk da haka akwai bukatar gwamnati ta zauna da mu ta yadda za a kawo gyara a cikin lamarin amma ba kawai rana-tsaka a ce an soke gudanar da wadannan makaratu ba. Babu wata gwamnati da ta taba kiranmu domin ta kawo mana gyara,” inji shi.

Wani dalibi da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Ahmad Abdullahi Gombe, ya ce duk da cewa ba abu ne mai dadi ya sa iyayensu suka kawo su wurin ba, amma suna bakin cikin komawa gidajensu don tsoron kada su kara komawa ruwa. “Mu zuwanmu wurin nan sai godiya ga Allah domin mun karu da darasin rayuwa. A yanzu da aka ce za mu koma gida, da yawanmu wallahi ba mu so ba. Saboda mun fara gane gaskiya. Ba mu son idan mun koma gida abokamu su sake jan  mu cikin harkar shaye-shaye da sauran laifuffuka,” inji dalibin.

Shi ma wani dalibi da aka kwance shi a mari ya ce, “Duk da cewa a daure muke cikin mari amma hakan bai hana mu yin walwala ba, domin mukan zauna mu gudanar da harkokinmu cikin wasa da dariya da juna. A wani lokacin har mantawa muke yi cew a mari muke, domin muna yin komai kamar muna gaban iyayenmu, illa iyaka yawo ne kawai ba mu yi.”

Aminiya ta tuntubi Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Malam Auwalu Umar Sanda inda ya yi wa Aminiya karin haske game da tsarin da gwamnatin ke da shi wajen ajiyewa tare da gyara tarbiyyar yaran da suka kauce hanya.

“A nan Kano muna da wurare biyu, na farko akwai wurin ajiye yara wanda ake kira ‘Remand Home’ ana ajiye yaran da ba su kai shekara 18 da ba, wadanda kuma suka aikata laifuffuka daban-daban kamar sata ko kisa da sauransu. Kuma kotu ce take kawo su wurin saboda ba za a iya kai su kurkuku ba. Haka muna da wurin gyaran hali na Kiru wanda muke ajiye masu shaye-shaye. Wannan waje gaba dayansa mutum 200 yake iya dauka. A yanzu haka mun yaye kashi na shida, muna gab da zuba kashi na bakwai,” inji shi.

Iyayen yara da dama a cibiyoyin da aka sake su, sun nuna damuwarsu kan wannan mataki da ake dauka inda suka ce su da kansu suka kai yaran saboda kangarewa. Sun ce wadansu shaye-shaye suke yi wadansu daba, don haka bai kamata a sako su ba tare da sun koma cikin hayyanciinsu ba. bukatar

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya