✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya ta tallafa wa Asibitin Hausawa

Asibitin Gwamnati da ke Unguwar Sabo a birnin Ibadan mazaunin Hausawa ya samu tallafin kayan aiki da suka hada da na’urorin gwajin jini da gadaje…

Asibitin Gwamnati da ke Unguwar Sabo a birnin Ibadan mazaunin Hausawa ya samu tallafin kayan aiki da suka hada da na’urorin gwajin jini da gadaje da katifu da bencinan zama don ganin likita da gyaran wutar lantarki wanda Gidauniyar Garin Na-Garke ta bayar domin kula da lafiyar marasa galihu maza da mata da kananan yara.

Da yake zagayawa da Aminiya sassan asibitin, Dokta Salisu Mika’ilu da ke aiki a karkashin Gidauniyar Garin Na-Garke ya ce “Mun samu tallafin na’urorin gwajin jini ne daga jagoran gidauniyar, Alhaji Ali Nakamba wanda ya yi sayo su daga Turai, tare da aikin gyaran lantarki, yayin da mataimakansa suka samar da gadaje da katifu da bencina  da  kuma kudin sayen magani ga marasa galihu.”

Dokta Salisu Mika’ilu ya ce, “Kashi 70 cikin 100 na mata masu juna biyu da suke zuwa asibitocin kudi a Ibadan yanzu garabasa ta samu gare su dalilin daukaka darajar aasibitin da Gidauniyar Garin Na-Garke take yi wajen horar da nas-nas da ungozoma da wadata su da kayan aiki.”

Aminiya ta samu zantawa da jagoran gidauniyar Alhaji Ali Nakamba wanda ya jinjina wa jaridar Aminiya kan kokarin da take yi wajen daukaka martabar harshen Hausa inda ya ce “Muna saya wa ’ya’yanmu wannan jarida ta Aminiya suna karantawa suna tsintar wasu kalmomin Hausa da suke neman bacewa a tsakanin mutanenmu a wannan sashi. Wannan ne dalilin da ya sa gidauniyar Garin Na-Garke ta fara tunanin yiwuwar koyar da harshen Hausa a cikin makarantun Islamiyya na wannan unguwa.”

“A kan ci gaban da muka samu a cikin wata uku da kaddamar da gidauniyar sai godiya domin abu na farko shi ne samun hadin kan jama’armu ’yan Arewa da ke zaune a Unguwar Sabo inda muka zama tsintsiya madaurinki daya. Ina  kira ga mutanenmu masu hannu da shuni su zo mu hada kai kamar yadda wasu kabilu suke yi wajen taimakon juna domin a nan aka haife mu a nan muka yi rayuwa daga kuruciya zuwa yanzu,” inji shi.

“Muhimmin abu na biyu kuma shi ne ina fata kana sane da cewa mun kirkiro gidauniyar ce domin taimaka wa jama’armu marasa galihu a kan ilimi da kiwon lafiya kuma hadin kan da muka samu ne ya kai ga nasarar samun gudunmawar kayan aiki da mutanenmu mazauna kasashen Turai da cikin gida Najeriya suka aiko mana da su muka yi amfani da su wajen daukaka darajar wannan asibiti.” inji shi.

Ta bangaren ilimi kuwa, Alhaji Ali Nakamba ya ce “Muna nan mun fara daukar nauyin biyan kudin makarantun firamare na kananan yara da saya musu littafai da riguna inda za mu ci gaba da yin haka har zuwa nan gaba da za a dauki nauyin karatunsu zuwa gaba.”

A game da alkawarin da wadansu ’ya’yan gidauniyar da ke aikin gwamnati da kamfanoni a sassa daban-daban suka yi na bayar da wani kaso daga cikin albashinsu a kowane wata don tallafa wa gidauniyar sai Ali Nakamba ya ce “Wannan shi ne babbar matsalar da muka fara fuskanta domin dole ne mu bude wa gidauniyar asusun ajiyar banki da za a rika tura kudi a ciki wanda har zuwa yanzu ba mu kai ga yin haka ba. Dukkan wadanda suka yi mana alkawari mun ba su shawarar su dakata tukunna sai idan mun yi wa gidauniyar rajista da bude mata asusun ajiya na kanta a banki.”