Search
Subscribe
Gidauniyar Daily Trust ta horar da ’yan jarida a Abuja

Mahalarta taron horarwar

Gidauniyar Daily Trust ta horar da ’yan jarida a Abuja

A farkon makon nan ne Gidauniyar Daily Trust da hadin gwiwar Gidauniyar MacAuthur ta fara horar da ’yan jarida sanin makamar aiki a kan binciken kwa-kwaf ta hanyar daukar hoto.

Taron horarwar wanda  ’yan jarida 28 daga kafofin watsa labarai daban-daban suka halarta da tare da editoci da wadansu daga kungiyoyi masu zaman kansu, ya gudana ne daga ranakun Talata zuwa jiya Alhamis a otel din Links da ke yankin Utako, Abuja.

Da yake jawabi a wajen bude taron horarwa, Shugaban Gidauniyar Daily Trust, Malam Wada Maida ya ce an shirya horon ne da tallafin Gidauniyar MacAuthur.

Ya ce gidauniyar ta shirya tarurrukan kara wa juna sani da horo ga ’yan jarida a shekara uku da suka gabata kyauta, inda suka dauko masu horarwa daga kasashen duniya da suka hada da Turai da Afirka ta Kudu da  Asiya da kuma wasu daga cikin Najeriya.

“Tallafin da Gidauniyar MacAuthur ke ba mu domin gudanar da wannan horo shi ne domin a tabbatar da cewa kun koyi abin da ya kamata don gudanar da binciken kwa-kwaf domin tabbatar da cewa gwamnati na yin aikin da ya kamata,” inji shi.

Ya kara da cewa horon zai taimaka wajen koyar da mahalarta sababbin dabarun harkokin sadarwa da suka kunshi daukar hoto, saukaka bayani ta hanyar fasahar zamani da sauransu.

“Yanzu daukar hoto ya zama babban abu a wannan aikin na jarida, musamman hada bayanai cikin hoto ko zayyana inda za ka ga an hada bayanai da yawa cikin hoto daya da bayani gamsasshe,” inji shi

A jawabin, Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Media Trust, Malam Mannir Dan-Ali ya bukaci mahalarta taron su dage wajen koyon sababbin dabarun da za a koya musu domin tafiya da zamani a harkar aikin jarida.

Dan-Ali ya ce hoto mai kyau yana taimakawa wajen isar da sako da jawo hankalin masu karatu, inda ya ce duk dan jarida da ya rika tafiya da zamani zai dade ana yi da shi a aikin.

Sai ya ce ba dole manyan mutane da ’yan siyasa za a rika dauka a hoto ba, inda ya ce dan jarida na kowa ne.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin