✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar kungiyar Izala ta ba marayu da zarawa tallafi

Gidauniyar marayu da zawarawa a karkashin kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah, reshen Jihar Oyo, ta bayar da tallafin turamen shadda da atamfa da kudin…

Gidauniyar marayu da zawarawa a karkashin kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah, reshen Jihar Oyo, ta bayar da tallafin turamen shadda da atamfa da kudin dinki don salla ga marayu da zawarawa 558.
Gidauniyar, wacce ta tara gudunmawar fiye da Naira miliyan daya da dubu dari uku da turamen shadda da atamfa daga bayin Allah na rassan kungiyar JIBWIS da ke Sabo da Bodija da Akinyele da Sasa da Ojo, wadanda ta rarraba su ga marayu 163 da zawarawa 385.
Sheikh Aliyu Muhammed Sani Adarawa, wanda hedkwatar JIBWIS ta kasa ta aika don karatun tafsirin watan Ramadan na bana a jihar, tare da tallafin shugaban kungiyar na jiha, Ustaz Salisu Abdullahi da Uban kungiya, Magajin Garin Bodija, Alhaji Musa Mai Buhu, su ne suka jagoranci rabon tallafin, a ranar, wadda ta zo daidai da ranar rufe karatun tafsirin na bana.
Da yake jawabin rufe karatun, Sheikh Aliyu, wanda shi ne shugaban majalisar malaman kungiyar JIBWIS a Jihar Neja, ya ja hankali kan a kula da muhimman darussa da majalisin ya karantar, musamman bauta wa Allah Shi kadai ba tare da hada shi da wani a cikin bautar ba da yin bautar a kan tsarin koyarwar ManzonSa da kyautata mu’amala da mutane wajen kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma biyayya ga shugabanni.
Dangane da gidauniyar kuwa, malamin ya bukaci al’ummar musulmi su taimaka wa marayu da zawarawa domin su sami saukin gudanar da kyakkyawar rayuwa.
Shugaban kungiyar na Jihar Oyo, Ustaz Salisu Abdullahi ya yi murna ne da samuwar nasarar gidauniyar, wacce shugaban kungiya na kasa, Sheikh Bala Lau ya umarci kowane reshen kungiya ya bude. “Wannan gidauniya ta dukkan musulmi ce, ba maganar Izala ba ce, ya kamata kowa ya bayar da gudunmawa, musamman saboda marayu da zawarawa za a lura da su. A nan jihar kawai mun fara samun marayu fiye da 1,000 da masu rikonsu suka kawo mana su domin samun wannan tallafi tare da zawarawa masu yawa”. Inji shi.
Shi kuma shugaban kungiyar JIBWIS, reshen Bodija Ibadan, Alhaji Muhammed Sani dandare Jega jinjina wa al’ummar musulmin Bodija ya yi ganin sun bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansu ta fannin bayar da gudunmawa mai tsoka ga gidauniyar, wadda ya yi fatan dorewarta har abada.