✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Zakka da Wakafi ta koya wa mata 100 sana’o’i a Gombe

A kokarinta na taimaka wa marasa galihu da rage zaman kashe wando, Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Gombe ta koya wa mata 107 sana’o’in hannu…

A kokarinta na taimaka wa marasa galihu da rage zaman kashe wando, Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Gombe ta koya wa mata 107 sana’o’in hannu don su dogara da kansu wajen kula da kansu da marayun da aka bar musu.

A zantawarta da Aminiya, daya daga cikin masu koya wa matan sana’a, Malama Maryam Yaya, wadda aka fi sani da Maman ’Yan biyu ta ce suna koya wa matan yadda ake hada kayan kanshi ne irin su turaren Humra da na sawa a jiki da na daki da turaren wuta da sauransu don su samu madogara a rayuwa.

Malama Maryam Yaya, ta ce mata marasa galihu  da suka zakulo suka koya wa sana’ar su ne wadanda mazansu suka rasu suka bar su da yara da kuma wadanda ba su da gata.

Ta ce Gidauniyar Zakka da Wakafi an kafa ta ce da zakkarda mutane suke bayarwa da kuma wakafi da ake samu.

A cewarta, matan suna bada hadin kai wajen koyon sana’ar, saboda sun ga ribar sana’a domin tun yanzu suna yin kayan suna sayarwa kuma ana saye.

Maryam Yaya, ta bai wa matan shawarar su kara himma wajen yin kayayyakin da kyau domin dogaro da kai ta yadda nan gaba za su taimaki wadansu.

Daya daga cikin matan da suka koyi sana’ar, Lami Abdullahi daga Unguwar Alkahira, wadda take da marayu biyar cewa ta yi ta amfana sosai da tallafin koyon sana’ar. Kuma  an ba su jarin Naira dubu 10 kyauta kuma an koya musu sana’a  ba tare da sun biya ba.

Ta ce ta samu rufin asiri, inda duk mako biyu suke zuwa ana kara yi musu bita kuma ribar da suka samu suna raba ta uku su dauki daya su kara daya a kan uwar kudi, sannan su kai kashi daya ana ajiye musu idan ya taru za a ba su kudinsu a kuma kara musu jari wanda ake kiran wannan ajiya asusun gata.

Ita ma A’isha Ibrahim Adamu da take Unguwar Jauro-Kuna da mijinta ya rasu ya barta da ’ya’ya cewa ta yi da wannan tallafi na zakka da wakafi take yin awara da zobo a gida amma yanzu da ta samu tallafin tana yin kayan kanshi da zanen gado da sauransu, danta da ya bar makaranta a baya yanzu ta mayar da shi.

Sai ta bai wa matan aure shawarar cewa su rika yin sana’a komai kankantarta saboda za ta taimaka musu wajen rage wasu matsalolin gida, idan kuma Allah Ya jarrabe su da rasuwar miji ba za su shiga kuncin rayuwa saboda rashin abin yi ba domin sun riga sun saba da dawainiya.

Matan dai suna samun horo ne na tsawon mako biyu kuma a watan Disamba ko Janairu mai zuwa ne za a yaye kashi na daya da na biyu da na uku da suka koyi sana’o’in.