✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gimbiya Sadiya Sanusi Lamido Sanusi: Mai hakuri na tare da riba

Gimbiya Sadiya Sanusi Lamido Sanusi ‘yar Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Dokta Ado Bayero ce, sannan uwargidan  dan Majen Kano kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya,…

Gimbiya Sadiya Sanusi Lamido Sanusi da jikantaGimbiya Sadiya Sanusi Lamido Sanusi ‘yar Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Dokta Ado Bayero ce, sannan uwargidan  dan Majen Kano kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ce. A wannan hirar, ta gaya wa Zinariya yadda rayuwar gidan sarauta take, da kuma yadda take lura da iyalinta. A sha karatu lafiya:

Tarihina
Assalamu alaikum warahmatullah, sunana Sadiya amma a gida ana kirana da Bagadede. Na yi karatun farimare a Gidan Sarki Primary School, sannan na yi makarantar Sakandaren ‘Yan mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) a Kazaure da yanzu take Jihar Jigawa, daga nan kuma na yi Jami’ar Bayero da ke Kano. Ni ce ta 16; a mata kuma ta 7. Mu 62 ne a gidanmu.
Abin da ya faru da ni ina karama da ba zan manta da shi ba
Ba a gaya mana lokacin da za a daura mana aure a gida, domin zan iya tunawa ina da shekara 15 a lokacin ina sakandare a Kazaure, sai kawai kanina ya zo makarantar a Kazaure ya sanar da ni cewa za a daura mini aure. An daura mini auren a Kazaure. Sarkin Kazaure Ibrahim Adamu ne ya daura mini aure. A lokacin da na ga kanina sai hankalina ya tashi, na ce masa “lafiya”? Sai ya ce “Zuwa aka yi a daura miki aure”. Na san za a yi mini aure amma ban san lokacin ba tun da ba tambayarka yaushe za ka yi aure za a yi ba. Tabbas ba zan manta da wannan ba.
Yadda na hadu da maigidana
To maigidana dai dan uwana ne, kuma a gida ya tashi. Mun tashi tare, da ji nake ma yayana ne, saboda kullum yana tare da ‘yan uwana maza, su ci abinci tare, su kwanta tare. Na tashi na gan shi a gidanmu. Shekararmu 25 yanzu da aure.
Rayuwa a gidan Sarauta
A gaskiya, gidan sarauta (fada) daban yake da sauran gidaje. Mun tashi da ‘yan uwanmu da kakanninmu da kannen babanmu da dogarai a cikin fada. Gida ne mai jama’a da yawa. Kamar duniyarmu ce a cikin fada saboda ba ma fita. Kamar yadda na ce muku na yi makaranta a ciki, muna da asibiti da kotu. Muna da komai a ciki. Mukan yi biki a ciki, hatta in wata ba ta da lafiya ba inda muke fita.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina. Mahaifina kamar abokina ne, domin a lokacin da nake karama, ina da surutu kuma nakan ba da labari. Duk abubuwan da ya faru a gida, nakan je na ba shi labari. To shi ya sa ma gaba daya ba mu cika shiri da mahaifiyata ba, saboda nakan kai masa labarin da ya kamata da wanda bai kamata ba don yaranta.
Halayen da na koya daga iyayena
Gaskiya dai na koyi hakuri daga wajen mahaifina. Kuma mutum ne mai kawaici. Kawaici kuma na daga abin da na koya daga mahaifina. Ba na barin abubuwa su dame ni. Ina da kokarin fitar da abubuwa daga raina balle ma su dame ni. Na tabbata sarki haka yake. Yana da hakuri. Kuma ya taka gaya mini, bai taka kwanciya ya kasa barci ba, sai ranar da mahaifiyarsa ta rasu, saboda ba ya ajiye komai a ransa, wanda hakan kuma na nuna hakuri. Idan ka yafe wa mutum, to ba za ka kwana da shi a cikin ranka ba, ma’ana za ka manta da shi.
Abinci
Da yake na tashi a gidan gargajiya, na fi sha’awar abincin gargajiya da kuma girka shi. Ina son waina da sinansir da finkasau da tuwo.  Gaskiya ban cika sha’awar abincin turawa ba.
Tufafi
Ina sanya atamfa kodayaushe. ‘Ya’yana kullum sai su rika cewa na cika son sa atamfa. Idan na sa atamfa na fi ganin kaina a matsayin Bahaushiya. Kullum na fi son na tafi a kan al’adata.
Farin ciki
Abin farin cikin da ya taka faruwa da ni shi ne, lokacin da aka nada maigidana sarautar dan Majen Kano. Saboda  mun dade muna sa ran za a ba mu, daga karshe kawai ba ma tsammani sai aka ba mu. Sarautar dan Maje da aka nada maigidana ta sanya ni farin ciki.

Farin cikin zama uwa
Alhamdulillahi shi da kyauta ce daga Allah. Duk wanda Allah Ya ba ‘ya’ya dole ya yi farin ciki, kuma an ba shi amana. Kamar lokacin da na yi aure na dade ban haihu ba, na yi kamar shekara uku, kuma duk wanda aka yi mana aure tare da su, mu wajen 7 aka yi mana aure, duk sun haihu. Ni kadai ce ban haihu ba. A lokacin da na haifi dana na farko, gaskiya na yi farin ciki sosai. Kuma kalubale ne ga iyaye, dole ne mu yi godiya sannan kuma mu ci gaba da tarbiyyar ‘ya’yanmu da nasiha gare su.
Sirrin zaman aure
Gaskiya hakuri  da kuma biyayya su ne sirrin zaman aurena. Dole a kullum mijinki ya kasance a samanki komai matsayinki, dole ki san cewa miji ne a sama, ki bi shi, sannan kuma ki yi hakuri da abubuwan da zai yi miki. Kamar yadda kika ga iyayenki suka zauna a gidajensu shekara da shekaru, yana cikin abubuwan da za ki duba ki yi hakuri, sannan kuma ki yi biyayya ga miji.
Burina
Mutum a gaskiya ba zai rasa buri ba, amma gaskiya ni Alhamdulillahi. Kamar yadda na ce miki na karanta Kimiyyar Koyarwa, to kullum burina a da in zama shugabar makarantar sakandare. Amma yanzu ina son in koma in ci gaba da koyarwa a makaranta. In ga dai na zama malama.
kasashen da na fi sha’awar zuwa  hutu
Ina son zuwa Afrika ta Kudu, saboda kasa ce da za ka ga kamar gida. Za ka ga mutane wadanda launin fatarmu daya da su, sannan kuma ga turawa, gidajensu irin namu, kuma wani wurin ba irin namu ba. Akwai abubuwa da suke sanya ni nishadi a can, suke kuma sa nake son zuwa Afrika ta Kudu. Akwai wuraren kallon abubuwan al’ajabi masu yawa, kamar duwatsu da koramu da ruwa da gandun daji da gidajen tarihi da sauransu, kuma al’adunsu na ba ni sha’awa sosai.