✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasar Filifins ta ci wuraren tarihin kasar

Muhimman wuraren tarihi da dama sun rushe a sanadiyyar girgizar kasar mafi muni da aka taba yi a tarihin Filifins, don a cewar Shugaban kasar,…

Masu aikin ceton rai a girgizar kasar FilifinsMuhimman wuraren tarihi da dama sun rushe a sanadiyyar girgizar kasar mafi muni da aka taba yi a tarihin Filifins, don a cewar Shugaban kasar, Benigno Akuino, ya shirya rangadin wuraren da girgizar kasar ta shafa. Shi ma Gwamnan Bohol. Edgardo Chatto, ya bayyana yadda babban ginin dakin taro na tsibirin ya rushe. dimbin gadoji da majami’u masu tsohon tarihi, tun zamanin sa kasar Sapain ta yi musu mulkin mallaka, wato a tsakanin shekarun 1500 zuwa 1600, duk sun rushe a biranen Bohol da Cebu.
Mutane da dama suka rasa rayukansu a wani mummunar girgizar kasa da aka yi a kasar Filifins. Sashen nazarin albarkatun kasa na Amurka ya bayyana girgizar kasar da aka yi a tsibirin Bohol, an samu dimbin asarar rayuka a kan tudun asa mai tsirrai.
Wasu kuwa sun rasa rayukansu ne a sanadiyyar gine-ginen da suka rusau, suka fada musu, a gundumar Cebu. Rahotanni sun bayyana cewa, girgizar kasar ta auku ne a lokacin dake gudanar da hutun kasa. Kuma gine-gine da dama, wadanda suka hada da coci-coci masu dimbin tarihi duk sun ruguzo.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa mutum 57 suka mutu a Bohol, wasu 15 sun rasa rayukansu a gundumar Cebu. An kuma bayyana girgizar kasar a matsayin mafi muni da ta auka wa birni mafi girma na biyu a kasar; an kuma samu rahoton aukuwar bala’in a tsibirin Sikuijor da ke makwaftaka da Bohol.
Akwai mutane da suka jikkata, inda a halin yanzu wadanda suka samu raunuka, ko laulayin rashin lafiya ke karbar magani a asibitoci.
An samu a kalla masunta biyar da suka rasa rayukansu, lokacin da ginin tashar jiragen rowan da ke kusa da inda suke yin su ta ruguzo, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito. Wasu mutane sun rasa rayukansu ne a loakcin da aka samu yamutsi da turmutsittsin jama a filin wasa na gundumar Cebu, a cewar jami’in bayar da agajin gaggawa na kasar, Neil Sanchez.
“A duk lokacin da aka samu aukuwar girgizar kasa, mutane sai su yi ta hanzari ficewa daga inda suke,” inji shi, kamar yadda ya bayyana wa AFP. Jami’an hukuma a Bohol da Cebu sun sanya dokar ta-baci a yankunansu.
Shi ma wani mutumin Birtaniya, Dabid benables da yake da zama a Cebu, har tsawon shekara bakwai, ya bayyana cewa wannan shi ne mafi muni a girgizar kasar da ya taba gani.
“Yana da matukar ban tsoro, a lokacin da gine-ginen gidaje ke rusowa ba tare da wani abu ya tare su ba,” inji shi. Ita ma Bonita Cabile, wani mazaunin Mandaue da ke birnin Cebu ya bayyana BBC, cewa girgizar kasar.