Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Girmama 12 ga Yuni ba zai rufe bakin tsanya ba

Girmama 12 ga Yuni ba zai rufe bakin tsanya ba

A ranar 12 ga Yunin bana ne Gwamnatin Najeriya ta fara gudanar da bikin Ranar Dimokuradiyya da nufin mayar da ranar abin girmamawa  domin tunawa da soke zaben marigayi Cif MKO Abiola na ranar 12 ga watan Yunin 1993 da gwamnatin soja ta yi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da dokar da ta mayar da wannan ranar ta zama Ranar Dimokuradiyya maimakon ranar 29 ga watan Mayu da ake yi duk shekara a kasar nan, wato ranar da sojoji suka mika wa farar hula mulki a 1999.

Daga yanzu an mayar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya, ranar  29 ga Mayu kuma  ba  ta da muhimmanci a duk shekara sai dai a shekarar da aka sake zabe domin a rantsar da sababbin shugabanni a wannan ranar, saboda tsarin mulki ya tanadi cewa wa’adinsu zai kare a wannan ranar ce.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta yanke shawarar girmama ranar 12 ga Yuni ne ga alama domin dadada wa al’ummar yankin Kudu maso Yamma, wato kabilar Yarbawa, wadanda tun a 1993 da gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben Cif Abiola suke ta tayar da kayar baya, kuma har bayan rasuwar Cif Abiola ba su bar wannan tunzurin nasu ba.

Sai dai kuma a iyakar fahimtata wannan karimcin da aka yi wa ranar 12 ga watan Yuni ba zai sanya al’ummar yankin Kudu maso Yamma su rika raga wa gwamnatin Buhari ba, domin shi dan Arewa ne kuma sun dade suna adawa da yankin Arewacin kasar nan, suna fakewa da zaben 12 ga Yuni ne kawai domin ci gaba da nuna adawarsu ga al’ummar yankin Arewacin kasar nan.

Sanin kowa ne cewa a lokacin zaben 12 ga watan Yunin 1993 al’ummar yankin Arewacin kasar nan sun fi zaben Abiola fiye da yadda ’yan kabilarsa Yarbawa suka zabe shi, domin hatta a Jihar Kano, jihar da abokin takararsa Bashir Usman Tofa ya fito, kuri’ar da Abiola ya samu ta fi ta Bashir Tofa, domin Abiola ya samu kuri’a dubu 169 ne da 619, a yayin da Bashir Tofa ya samu kuri’u dubu 154 da 809.

Hatta a Jihar Kaduna wadda ita ce ke bin Jihar Kano a wajen yawan masu kada kuri’a a yankin Arewa, ita ma Abiola ne ke kan gaba da kuri’a dubu 389 da 713,  yayin da Bashir Tofa ya samu kuri’a dubu 356 da 860.

Idan an lura za a ga cewa kuri’un da aka kada a Jihar Kano ba su da yawa, na Jihar Kaduna sun fi yawa, duk da cewa Bashir Tofa dan Jihar Kano ne amma hakan bai sanya Kanawa fitowa da yawa su zabe shi ba, hasali ma ’yan kadan din da suka fito sai suka zabi Cif Abiola maimakon dansu.

Haka kuma a baki dayan kasar mutane ba su fito zabe da yawa ba saboda a wancan shekarar an haramta wa tsofaffin ’yan siyasa tsayawa takara aka ce sai sababbin jinin ’yan siyasa kawai za su tsaya takara, saboda haka tsofaffi kuma jiga-jigan ’yan siyasa sai dai suka zama ’yan kallo ko kuma suka mara wa wadansu sababbin jini baya, dalilin da ya sanya ke nan su Abiola da Tofa suka yi tasiri.

Gaba daya kuri’un da Abiola ya samu a kasa baki daya shi ne, miliyan takwas da dubu 341 da 309, shi kuma Bashir Tofa ya samu kuri’u miliyan biyar da dubu 952 da 807, wanda ya nuna cewa sahihan kuri’un da suka samu gaba dayansu su ne miliyan 14 da dubu 293 da 396. Wato dai babu dan takarar da ya samu kuri’u miliyan 10 a cikinsu.

Haramta wa tsoffafin jini takara ya taimaka kwarai wajen rashin fitowar jama’a su yi zabe, sannan uwa uba kasancewar ’yan takarar guda biyu dukkansu Musulmi ne ya sanya al’ummar Musulmi, musamman na yankin Arewa rashin fitowa, domin suna ganin duk wanda ya samu nasara nasu ne. Duk da cewa Bashir Tofa dan Arewa ne, amma al’ummar Arewa suna matukar girmama Abiola saboda kasancewarsa mutum mai taimakon jama’a ga kyauta kamar ruwan sama kuma ya shuka abubuwan alheri da yawa a yankin Arewa. Wannan ya taimaka kwarai wurin sanya al’ummar Arewa nuna halin ko-in -kula da zaben, saboda duk ’yan takarar nasu ne.

Haka kuma tsarin zaben ’yar-tinki da aka yi amfani da shi a lokacin ya taimaka kwarai wajen hana manyan mutane fita su yi zabe, domin tsari ne da za a yi layi a bayan dan takara ko hotonsa, saboda haka za a  gane dan takarar da mutum ya zaba, kuma idan dan takarar mutum ya fadi za a yi wa magoya bayansa ihu. Wannan ya taimaka wajen rage yawan masu  kada kuri’a, musamman su yallabai.

Sannan kuma yankin Yarbawa ba su fito sosai ba, duk da cewa dansu na takara, saboda sun dauki Abiola a matsayin dan adawa ne, domin a Jamhuriya ta Biyu bai goyi bayan Cif Obafemi Awolowo ba, ya goyi bayan Alhaji Shehu Shagari ne, domin haka al’ummar Yarbawa suna ganinsa a matsayin dan barandan yankin Arewa ne, domin haka suka ki fitowa su mara masa baya.

Kamar yadda Sule Lamido ya bayyana ne cewa har ranar 11 ga watan Yunin 1993 Yarbawa ba su tare da Abiola, amma da aka yi zabe a ranar 12 ga wata, sai aka wayi gari ranar 13 ga wata Yarbawa sun kwace Abiola sun ce nasu ne.

Saboda haka da aka soke zaben 12 ga watan Yuni sai suka tayar kayar baya suka ce ba su yarda ba dansu ya ci zabe an soke, daga nan suka shiga kashe ’yan Arewa da ke yankinsu tare da kona dukiyoyinsu, kuma haka suka rika yi yi duk shekara idan ranar ta zagayo, sai a shekarun nan suka dan tsagaita.

Saboda a samu kwanciyar hankali sai gwamnatin Babangida ta mika mulki ga gwamnatin riko, inda ta dauko dan kabilar Yarbawa daga Jihar Ogun inda Abiola ya fito ta nada shi a matsayin shugaban gwamnatin riko, amma duk da haka Yarbawa ba su hakura ba.

Haka kuma domin a kara kwantar musu da hankali aka sake dauko tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo daga gidan yari, aka yi masa afuwa, aķa tsayar da shi takara, aka ce ya ci zabe, ya yi mulki shekara takwas, amma hakan bai sanya Yarbawa sun daina tunzuri ba.

Saboda haka wannan karamcin da aka yi wa marigayi MKO Abiola ta hanyar girmama ranar 12 ga Yunin kowace shekara ba zai sanya su sassauta daga adawar da suke wa al’ummar Arewa ba, domin suna ganin zamansu da ’yan Arewa a kasar nan babbar matsala ce.