✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Giwa ta kashe sojan Birtaniya a Malawi

Wata giwa ta kashe wani soja dan Birtaniya a lokacin da yake wani aiki na dakile masu farauta ba bisa ka’ida ba a kasar Malawi.…

Wata giwa ta kashe wani soja dan Birtaniya a lokacin da yake wani aiki na dakile masu farauta ba bisa ka’ida ba a kasar Malawi.

Mathew Talbot mai shekara 22 na ayarin 1st Battalion Coldstream Guards, na aiki ne a gandun dajin Liwonde National Park a ranar 5 ga watan Mayu lokacin da giwar ta kai masa hari.

Shugabansa Laftana Kanar Ed Launders ya ce Talbot mutum ne mai “kwazo da kuma son mutane.’’

Sakatariyar Tsaro Penny Mordaunt ta ce ya kware sosai a aikin nasa sannan yana da matukar karfin hali.

Ta kara da cewa, “Wannan mummunan lamarin da ya faru tuni ne na haduran da rundunar sojinmu ke fuskanta a kullum, a yayin da suke kokarin kare daya daga cikin dabbobin da suka fi barazanar bacewa a doron kasa daga mutanen da ke son su karar da su domin biyan bukatun kansu.’’

Fadar Kensington ta ce Yariman Cambridge yana rubuta wata wasika zuwa ga ’yan uwan Talbot domin yi musu ta’aziyya.

Talbot mutumin yankin West Midlands ne kuma yana kan aikinsa na farko da aka tura shi ne inda da lamarin ya faru.

Ayarin sojojin Birtaniya da kungiyar da ke tsare dazuka (African Park Rangers), suna tafiya ne cikin ciyawa wacce ta kai tsawon mita 2.1 – lokacin da suka tarar da wasu giwaye da ba su gani da farko ba.

Daya daga cikinsu sai ta kai wa sTalbot hari. Jim kadan sai ya mutu saboda raunukan da ya samu kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ya mutu ya bar mahaifinsa Steben da mahaifiyarsa Michelle, da ’yan uwansa mata Aimee da Isabel da kuma budurwarsa Olibia.