Da Dumi Dumi

Gizagawan Jihar Kaduna sun kai ziyara

Na Katsina sun kai tallafi

 

A makon jiya ne Gizagawan Jihar Kaduna suka kai ziyara fadar Mai girma Sarkin Rido da ke Karamar Hukumar Cikhun a Jihar Kaduna.

Shugaban Gizagawan Jihar Kaduna, Kabir Khalil Mantissa ne ya jagoranci tafiyar. Bayan an yi musu iso da Sarkin Rido, Alhaji Hamisu Haruna, nan take shugaban ya ci gaba da bayyana manufofin Kungiyar Gizago.

Sarkin ya yi na’am da manufofin tare da sa wa Kungiyar Gizago albarka, daga nan kuma ayarin ya wuce zuwa ga masu masaukinsu, Bagizage Jafar Ali Rido da Bagizage Murtala Mohammad Rido.

ADVERTISEMENT

Ziyarar ta samo asali ne daga wadancan Gizagawa da aka ambata, inda Mantissa ya ce mutane ne da suka jima suna ba da gudunmawa ga Kungiyar Gizago, shi ya sa suka ga dacewar a rika kai wa mambobin da ke nesa da fadar Jihar Kaduna ziyara, ta hanyar kiran taro a duk karshen wata, domin karin dankon zumunci da kuma ci gaba da yada manufofin ƙungiya.

A Jihar Katsina kuwa, Gizagawan jihar ne suka kai tallafi gidan marayu.

Gizagawan sun kai tallafin ne a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar ta JihaR, Malam Bello Buhari.

Da yake mika tallafin, ya ce kayan da suka kawo, daya ne daga cikin manufofin ƙungiyar na ba da tallafi ga marayu da gajiyayyu da wadanda ke gidajen yari.

A jawabin godiya shugabar masu kula da marayun ta yi godiya matuka tare da yaba wa Kungiyar Gizago.

***

A labarin jajantawa kuwa, Bagizage Alhaji Yunus Abdullahi Kogi (0803 606 6547), Allah Ya yi wa yayansa rasuwa.

Bagizage Adamu Yahaya Gombe (0806 225 3727), dansa ne Allah Ya yi wa rasuwa.

Haka shi ma Malam Yahaya Usman Maikatifa (09033910639), Baffansa ne ya rasu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya