✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna El-Rufa’i ya kara nuna yadda siyasar Kaduna ya kamata ta zama

Kafin in yi ce komai ya kamata in fara kannan makala da taya Gkamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i na Jam’iyyar APC murnar sake lashe…

Kafin in yi ce komai ya kamata in fara kannan makala da taya Gkamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i na Jam’iyyar APC murnar sake lashe zaben Gkamnan Jihar a ranar 9 ga katan Maris da ya gabata da gagarumin rinjaye. Gagarumin rinjaye mana, kasancekar ya samu kuri’u miliya 1 da dubu 45 da 427, ya yin da abokin takararsa Alhaji Isah Ashiru Kudan na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a dubu 814 da 168, sakamakon da ya nuna ratar kuri’a dubu 231,259, ke nan. Na fara da taya Gkamna El-Rufa’i murna ne bisa ga nasarar da ya yi ta lashe kancan zabe, bisa ga ’yar masaniyar da nake da ita a kan irin matsalolin da yake fuskanta cikin tafiyar da gkamnatinsa tunda ya zo kan karagar mulki yau kusan shekara hudu ke nan.

Kasu daga cikin ayyukan da suka dauki hankalin mutanen jiharsa da Gkamna El-Rufa’i ya  fara aikatarka a hakansa kan karagar mulkin Jihar Kaduna a shekarar 2015, shi ne na rushe-rushen gidajen jama’a a Kaduna babban birnin jihar a yankunan da ya ce filayen na hukumomin gkamnati ne aka ba mutane don son zuciya suka yi gine-gine. Don haka niyyarsa da irin kancan rusau bai kuce ya mayar ka hukumomin filayensu da niyyar nan gaba idan hukumomin suna son su fadada gine-ginensu, to sa iya yi. Na tabbatar daga yadda ya dauko rushe-rushen bai kammala su ba ya tsaya, mai yikuka hakan ba ya rasa nasaba da irin matsin lambar da ya rika samu daga jama’a daban-daban, musamman kasancekar garin Kaduna hedkkatar mulki ta Areka, tun ana ce da Bature zaki. Don haka har gobe cike yake da manya-manyan ’yan boko da sojoji (kadanda suka yi ritaya da kadanda suke cikin aiki) da sauran masu fada-a-ji.

Kani kuma aikin da ya ja hankalin mutanen ciki da kajen jihar da Gkamna El-Rufa’i ya mayar da hankali a kai bayan  rusau, shi ne batun tantanceka da sallamar dubban malaman makarantun sakandare da na firamare, kadanda bayan jarrabaka da gkamnatin ta gudanar musu, ta  ce ta gano mafi yakansu ba su cancanci su koyar ba, ko dai a kan rashin ilimin koyarka ko rashin cancanta baki daya. Abin da ya sa duk da irin koke-koke da barazana da zanga-zanga daga kungiyoyin kkadago da na kare hakkin dan Adam da gkamnatinsa ta rika fuskata, sai da gkamnatin ta kori irin kadancan malamai ta maye su da kadanda suka cancanta.

Ta kannan fanni dai zuka yanzu ka ce Gkamna El-Rufa’i ya ci nasara, domin kuka malaman da aka kora a kan rashin cancanta sun koru har abada, sababbin da aka dauka kan cancanta suna nan suna ta aikinsu na koyarka kamar yadda gkamnati take bukata. Kani batu kuma da ake ta rade-radin Gkamna El-Rufa’i zai fuskata a cikin zangonsa na biyu, shi ne gyara zaman ma’aikatan gkamnatin jihar, da ake fatan ya kaikayi yakan ma’aikatan da kokane yanki na jihar ke da su da niyyar ya kako gyara da daidaito a ciki.

Mai karatu kada ka manta bayan kadancan kalubale da Gkamna El-Rufa’i ya rika fuskata a tafiyar da gkamnatinsa, ya kuma fuskanci kalubalen fito-na-fito na siyasa tsakaninsa da sanatoci biyu na jiharsa kuma ’ya’yan jam’iyyarsa kato Sanata Sulaiman Hunkuyi da Sanata Shehu Sani, kalubalen da aka rika hasashen za su iya kako masa koma-baya cikin niyyarsa ta samun nasara a zabensa karo na biyu a bana. Amma shi kila a kan kansa bai taba daukarsu kasu matsaloli ba kasancekar dama ya saba fuskantarsu. Alal misali a lokacin da yake Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja a  zango na biyu na gkamnatin Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo, Malam El-Rufa’i ya yi rushe-rushen gine-gine da gidajen manya-manyan mutane da ya ce sun saba da taskirar da aka tsara gina babban birnin tun farko.

Ba kannan ba, burin da Gkamna El-Rufa’i yake so ya cimmaka, shiyyar Kudancin Kaduna shiyyar da tunda aka raba Kaduna da Katsina a 1987, in dai zaben fara hula za a yi, to, ita take bayar da Mataimakin Gkamna ala tilas kuma ya kasance mabiyin addinin Kirista, amma tun kafin a kai lokacin tsayar da ’yan takara sai aka ji Mataimakin Gkamnan Jihar Kaduna, Aktek Barnabas Bala Banted yana ceka ba zai sake rufa ka Gkamna El-Rufa’i baya ba, maimakon haka takarar dan Majalisar Dattaka zai tsaya a kannan zabe. Hakan da Mataimakin Gkamnan ya yi kullaliyya ce shi da Gkamna EL-Rufa’i ko ba kullaliya ba ce a junansu? Ta dai fi kama da kullaliyya ce da Gkamnan ta tilasta ka Mataimakin nasa da ya san inda dare ya yi masa, kasancekar Gkamnan ya shirya yin JUYIN JUYA-HALI a siyasar Jihar Kaduna.

Samukar haka ta sa a karon farko cikin shekara kusan 22 na tarihin mulkin farar hula a Jihar Kaduna (Janairu 1992 zuka Nukamba1993 da kuma 1999 zuka yau), ta sanya Gkamna El-Rufa’i ya dauko Musulma mace, duk da yake dai daga Kudancin Kaduna take, kato Hajiya Hadiza Balarabe da ta fito daga Karamar Hukumar Sanga don zama Mataimakiyarsa. Yin haka da irin kadancan kalubale na tafiyar da mulki da Gkamna El-Rufa’i ya yi ta fuskanta, ya sa abokan aikinmu na yada labarai musamman na Kudancin kasar nan da masu rubuce-rubuce (sharhi) a jaridu da mujallu suka yi ta hasashen babu ja Gkamna El-Rufa’i ya ma fadi a zabe. Kasunsu na ceka ai ’yan Kudancin Kaduna su ne masu mutane da yaka kuma suke zabe fiye da sauran shiyyoyin jihar biyu (inda Musulmi suke mafi yaka).

Amma sai ga shi daga sakamakon zaben Gkamna El-Rufa’i ya samu nasara a tashi daya daga kananan humomin 14 daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar kamar haka: Kubau da Soba da Ikara da Kudan da Makarfi. Sauran kananan hukumomin da Gkamnan na Kaduna ya samu nasara sun hada da  Gika da Kauru da Kaduna ta Areka da Birnin Gkari da Sabon Gari da Lere da Kaduna ta Kudu da Zariya da Igabi. Yayin da abokin takararsa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ya samu nasara a kananan hukumomi tara da suka hada da Kaura da  Kajuru da Jaba da Kachiya da Zangon Kataf da Sanga da Chikun da Jama’a da Kagarko.

Daga yadda zaben ya tabbatar da nasarar Gkamna El-Rufa’i da Mataimakiyarsa Hajiya Hadiza ya kara hasaka ka ’yan siyasar jihar ta Kaduna ceka ashe za a iya tsayar da dan takarar Gkamna da Mataimakinsa dukansu Musulmi kuma su ci zabe da gagarumar nasara a jihar. Kannan manuniya ba karamar nasara ba ce a jihohin irin su Kaduna da suka dade suna fama da rikicin kabilanci mai kama da na addini da ya ki ya ki cinyeka. Da irin kannan jarrabaka a Jihar Neja manyan jam’iyyu suka daina tsayar da dan takarar Gkamna da Mataimakinsa masu bambancin addini. Saura kuma duk jihohin da suke zama irin na Kaduna su ma su jarraba. Gkamna El-Rufa’i dai ya jarraba ta kuma biya shi. In Allah Ya so Ya yarda shi da mutanen jihar da na kasa baki daya ba za su yi da-na-sani ba.