✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta haddasa babbar asara a Kasuwar Kurmi

Fiye da shaguna 60 ne suka kone kurmus sakamakon tashin wata gobara a sashen masu sayar da leda da kuma kayan kamshi a Kasuwar Kurmi…

Fiye da shaguna 60 ne suka kone kurmus sakamakon tashin wata gobara a sashen masu sayar da leda da kuma kayan kamshi a Kasuwar Kurmi da ke Kano.

Aminiya ta gano cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 3 na daren ranar Lahadin da ta gabata, wanda kuma ba a sami nasarar shawo kanta ba har zuwa karfe 8:30 na safiyar ranar Litinin. Kuma an yi zargin cewa gobarar ta tashi ne sanadiyar dawo da wutar lantarki cikin dare a kasuwar.

Mafi yawan ‘yan kasuwar da Aminiya ta tatatuna da su sun zargi Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, inda suka ce jami’an hukumar ba su kawo musu dauki akan lokaci ba.

Wani mai sayar da leda a kasuwar, Malam Sani Ali wanda dukkan shagunansa guda shida suka kone a gobarar ya bayyana cewa “Lokacin da muka sanar da Hukumar Kashe Gobara ba su zo a kan lokaci ba inda suka nuna mana cewa wai motarsu ba ta da batir. Mu muna ganin hakan gazawa ce babba. domin ko a kwanakin baya sai da ‘yan kasuwarmu suka saya wa ofishin hukumar da ke Jakara batirin mota”

Jami’in Hulda da Jam’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Muhammad Kabir Sa’id ya musanta batun rashin halartar jami’ansu akan lokaci, inda ya ce sun sami sako akan tashin gobarar da misalin karfe 4 na daren ranar Lahadi wanda kuma a take jami’ansu suka isa wurin don yin abin da ya kamata.

Game da batun korafin ‘yan kasuwar akan sayen batirin motar jami’in ya ce ba zai iya cewa komai akai ba sai har idan an gudanar da bincike.