Da Dumi Dumi

Gobara ta kashe jarirai 8 a asibiti a Aljeriya

A safiyar yau Talata rahotanni na bayyana cewa, a kalla jarirai 8 ne suka mutu yayin da gobara ta tashi a wani asibiti a kasar Aljeriya.

Hukumar bada agajin gaggawa ta sanar da cewa, gobarar ta tashi ne a asubahin yau a asibitin da ke garin Oued Souf kimanin nisan Kilomita 700 na Kudu maso Gabas na babban birnin Algiers.

Jariran sun mutu ne sakamakon konewa da suka yi wasu kuma saboda hayakin da suka shaka. An ceto yara 11 da wasu mutum 65  tare da mata 37 lokacin tashin gobarar.

Share