Da Dumi Dumi

Gobara ta lakume kayan agaji a Kalaba

A karshen makon da ya gabata ne gobara ta lakume dukiya ta milyoyin Nairori a ofishin ajiye kaya na Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kuros Riba wato SEMA.

Kayayyakin dai hukumar da ke kula da tashohin jiragen ruwa da kuma bayar da tsaro wato NIMASA ce ta bayar da su gudunmuawa domin raba su ga ‘yan gudun hijirar Ambazoniya da ke sassa daban-daban na wasu kanana hukumin jihar Kuros Riba.

Mukaddashin hukumar Princewill Ayim ya bayyanawa manema labarai cewa, ”Tun lokacin da aka kawo mana kayan taimako domin mu raba muka fara raba su, mun ba wadanda ke sansanin ’yan gudun hijira da ke Bakassi kuma har na samarwa sauran sansanin da ke garin Biase da Ogoja kafin wannan gobarar ta tashi“. In ji shi.

Wakilin Aminiya ya tambayi mukaddashin hukumar bayar da agajin musabbabin tashin gobarar sai ya ce, ”Muna kyautata zaton barayi ne  suka shiga ta tsakanin na’ura mai sanyaya daki suka kutsa ciki suka cinna wutar da nufin yin sata“.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, ”Bayan sun balle katakon da aka makala a na’urar sai suka yi amfani da wadannan katakon suka kunna wuta suka sanya wa ragowar kayan wuta sannan suka saci na sata.”

ADVERTISEMENT

Da taimakon jami’an kashe gobara ne aka yi nasarar kashe wutar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya