Search
Subscribe
Gobarar tankar mai ta lakume shaguna a Onitsha

Gobarar tankar mai ta lakume shaguna a Onitsha

Wata tankar man fetur ta kamfanin Premium Motor Spirit (Petrol), ta kama da wuta a garin Onitsha, jihar Anambra. Motar wanda take dauke da man fetur ta kama da wuta ne bayan ta fadi a hanya lokacin da take tafiya.

A yayin hada wannan rahoton ba a sanar da rasuwar wani ba lokacin aukuwar gobarar.

Wakilinmu ya bayyana cewa, gobarar ta faru ne a yammacin yau Laraba a yankin unguwar Upper Iweka, gobarar ta lakume wasu wuraren kasuwanci na yankin.

Wani ganau ya bayyana cewa, gobarar ta kai har zuwa kasuwar Ochanja inda ta yi sanadiyyar kone wasu shaguna da wasu yankunan birnin.

Wasu shaguna da gobarar ta lakume
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin