✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Najeriya za ta yi ango

A gobe Asabar ce ’yan Najeriya masu jefa kuri’a za su fita rumfunan zave a sassan kasar nan don zaven wanda zai zame angon Najeriya…

A gobe Asabar ce ’yan Najeriya masu jefa kuri’a za su fita rumfunan zave a sassan kasar nan don zaven wanda zai zame angon Najeriya na tsawon shekara hudu masu zuwa. Manyan ’yan takara biyu da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamo angon su ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP. Manyan ’yan takarar dai sun kammala zagayen kamfe dinsu a jiya Alhamis.

Miliyoyin ’yan Najeriya masu shekara 18 zuwa sama da suke da katin zave ne za su kada kuri’a domin zaven Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa.

Akwai ’yan takara akalla 73 wadanda jam’iyyun siyasa 73 daga cikin 91 da ake da su a Najeriya suka tsayar, inda za su fafata a babban zaven mafi muhimmanci a kasar nan.

Kuma a gobe din ne ’yan takara 1,800 za su fafata wajen neman kujerun sanatoci 109 da ake da su a Majalisar Dattawa da kuma ’yan takara 2,600 da za su fafata domin cike gurabe 360 na Majalisar Wakilai.

Cikin ’yan takarar Shugaban Kasa har da Shugaba mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari, wanda babbar jam’iyya mai mulki ta APC ta tsayar.

Sai kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar, wanda babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta tsayar.

Bayan wadannan ’yan takara biyu da suka yi fice, akwai wadansu da dama da wasu jam’iyyun siyasa suka tsayar. Cikin su har da su DOkta Adesina Fagbenro-Bryon na Kowa Party da Rabaran Chris Okotie na FDP da Gbenga Olawepo Hashim na Peoples Trust da Hamisu Santuraki na MPN da Cif Sam Eke na GPN da Dokta Olapade Agoro na NAC da Edozie Madu na Independent Democrats da  Elda Williams Olusola Awosola na DPC da Usman Ibrahim Alhaji na NRM da kuma Misis Oby Ezekwesili na ACPN.

Sauran sun hada da Alhaji Ahmed Sakil na UPN da Yarima Ike Keke na NNPP da Mista Isaac Babatunde Ositelu, na Accord Party da Manjo Janar John W.T Gbor na APGA da Dokta Olusegun Mimiko na ZLP da Dokta Nicholas Felid na PCP da Breakforth Onwubuya na FJP.

Akwai kuma Apostil Sunday Chukwu Eguzolugu na JMPP da Mista Donald Duke na SDP da Manjo Hamza Almustapha na PPN da Dokta Obadiah Mailafia na ADC da Dokta Rabia Cengiz ta NAC da Alhaji Isa Bashiru na ANDP da Omoyele Sowore na AAC da kuma Yusuf Sani Yabagi na ADP.

Sai Fasto Habu Aminchi na PDM da Malam Hussein Abubakar na MAJA da Tope Kolade Fasua na ANRP da Kingsley Moghalu na YPP da kuma Ahmed Buhari na SNP da sauransu.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewar jama’ar da suke da katin zave a fadinNajeriya su miliyan 84 da dubu 4 da 84, kamar yadda alkaluman hukumar zave suka nuna ne ake sa ran su fita zaven. Adadin ya nuna an samu karin masu kada kuri’a miliyan 14 da 281 da 734 kan adadin da ake da su kafin zavuvvukan da aka gudanar shekara hudu da suka gabata.

Hankalin duniya gaba daya ya dawo kan Najeriya domin ganin yadda za ta kaya a wadannan zavuvvuka da za a gudanar a kasar wadda take da jama’a kusan miliyan 200, wacce kuma ta fi daukacin kasashen duniya yawan bakar fata.

Tuni dai Hukumar Zave ta Kasa (INEC) a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu ta ce ta kammala shirye-shirye tsaf domin gudanar da wadannan zavuvvuka.

Wannan shi ne karo na shida da za a gudanar da manyan zavuvuka a Najeriya bayan da sojoji a karkashin tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalam Abubakar (mai ritaya) suka mayar da kasar karkashin tsarin dimokuradiyya shekara 20 da suka gabata.

Za a gudanar da zaven Shugaban Kasa a cibiyoyin zave sama da dubu 120 da suke mazavu sama da 8,000 a kananan hukumomi 776 na jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

 

Buhari ko Atiku

Duk da cewa akwai ’yan takarar Shugaban Kasa 73, hankalin ’yan Najeriya da masu sharhi kan al’amuran siyasa ya karkata ne kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Hakan yana da alaka ne da karfin da wadannan ’yan takara da jam’iyyunsu suke da shi game da zaven. Haka kuma ana ganin su ne ke kan gaba saboda tsarin karva-karva a tsakanin Arewa da Kudu da yawancin jam’iyyun 91 da ake da su suka yarda da shi.

Wadannan ’yan takara a jiya Alhamis ne suka kammala kamfe dinsu a jihohinsu na haihuwa, kamar yadda dokar zave ta ce tilas a kammala kamfe awanni 24 kafin tafiya rumfunan zave.

Buhari ya kammala nasa kamfe ne a jiharsa ta Katsina, inda daga can ne ya wuce mahaifarsa Daura domin kada kuri’arsa gobe.

Shi ma Atiku tuni ya gudanar da kamfe na karshe a garin Yola fadar Jihar Adamawa, kuma ana sa ran zai wuce garinsa na haihuwa wato Jada domin ya kada kuri’arsa.

Buhari da Atiku sun karade kasar nan baki daya a kwanaki talatin din da suka gabata inda suka gudanar da kamfe daga jiha zuwa jiha, tare da shaida wa magoya bayansu abubuwan da za su yi in har suka ci zabe.

A duk inda Shugaban Kasa Buhari ya je kamfe yana nanata cewa ya rike amanar da al’ummar Najeriya suka ba shi a shekara hudu da suka gabata.

Misali a gangamin kasa da ya gudanar a Birnin Tarayya, Abuja, a shekaranjiya Laraba, Shugaba Buhari ya ce zai ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, kuma zai ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya kuma zai ci gaba da kawo tsare-tsaren da za su dora tattalin arzikin kasa a kan alkibla mai kyau.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yana neman mulki ne ba wai don son zuciya ba, sai don ya gyara tsarin tafiyarta ta yadda talaka zai gani a kasa. Ya bayyana cewar Jam’iyyar PDP da mukarrabanta sun yi ta’adi sosai a shekara 16 da suka yi a madafun iko daga 1999 zuwa 2015; don haka ya ja kunnen ’yan Najeriya da kada su yi sake su bari PDP ta  dawo.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin fadada damar da matasa da mata suke da ita kan yadda ake gudanar da mulki, kuma zai kara ba da muhimmanci ga ayyukan gona da gyara hanyoyin mota, da na jirgin kasa da kuma wutar lantarki. Sa’annan ya ce zai gudanar da babban bincike kan yadda tsohon Shugaba Kasa Olusegun Obasanjo ya kashe Dalar Amurka biliyan 16 kan harkar wutar lantarki ba tare da an samu wani ci gaba ba.

Shi ma Atiku Abubakar wanda ya gudanar da babban taro a Legas ya nanata cewa in har ya hau kan madafun iko, zai sake fasalin Najeriya. Ya kuma yi alkawarin bai wa matasa da mata mukamai masu gwavi, ya ce zai sayar da matatun mai domin ’yan kasuwa su gyara su ta yadda Najeriya za ta rika samun kudin shiga.

Atiku ya yi alkawarin zai kawo sabon salon yaki da miyagun mutane; kuma zai gyara dokokin kasa ta yadda Turawa za su zo su zuba jari mai yawa a harkokin kasuwanci.

 

Gwabzawar karshe tsakanin Buhari da Atiku

Ga dukan alamu wannan ita ce gwabzawa ta karshe da Buhari da Atiku za su yi domin neman mulkin kasar nan.

Tsarin mulkin Najeriya dai ya bayar da damar yin shugabancin kasa sau biyu.

Don haka idan Buhari wanda ke da shekara 76 a yanzu ya sake samun nasara, to ba zai sake yin takara a zaven shekarar 2023 ba; domin tilas ya mika mulki.

Kuma a bisa tsarin karva-karva da jam’iyarsa ta APC ta yarda da shi, za su tsayar da dan takara ne daga yankuna uku da ake da su a Kudu (Kudu maso Yamma ko Kudu maso Gabas ko Kudu maso Kudu).

A wannan lokaci Shugaba Buhari zai cika shekara 80 cif a duniya; kuma tuni wasu na kusa da shi kamar Mataimakinsa Yemi Osinbajo, ya lasa wa yankinsa na Yarbawa zaki a baki, inda ya ce hakika mulki zai koma wajensu in har suka mara wa Buhari baya a wannan karo.

Shugaba Buhari ya yi takarar Shugaban Kasa har sau hudu kafin ya yi nasara. Ya fara neman shugabanci a shekarar 2003 inda Shugaba mai ci a wancan lokacin Cif Obasanjo ya kayar da shi. A shekarar 2007 ya sha kaye a hannun marigayi Umaru ‘Yar’aduwa; a shekarar 2011 kuma Goodluck Jonathan ya kayar da shi kafin ya rama a shekarar 2015.

Atiku wanda ke da shekara 72 a halin yanzu, ana ganin zai yi wuya ya sake takara in har bai kai ga gaci ba a wannan karon.

To sai dai in har ya yi nasara, zai iya kasancewa a kan madafun iko har zuwa shekarar 2028 lokacin da zai cika shekara 80 a duniya.

To sai dai in har bai samu a yanzu ba, to ana ganin mulki ya kuvuce masa ke nan domin bisa ga dukan alamu daga Kudu jam’iyarsa ta PDP za ta dauko dan takararta, ganin yadda ta tafka kuskure a shekarar 2015, lokacin da ta tsayar da Jonathan a matsayin dan takara maimakon ta dauko wani daga Arewa.

Idan har mulki ya koma Kudu inda zai dauki shekara takwas a can, to Atiku zai kasance yana da shekara 84 ke nan kafin ya sake dawowa Arewa.

Masu fashin baki suna ganin inhar da rai to zai yi wuya ya ce zai nemi mulki a wannan lokaci.

Duk da an yi hasashen cewa zaven bana ba zai yi zafi ba kamar na 2015, ganin cewa Buhari da Atiku duk Musulmi ne daga Arewacin Najeriya, alamu sun nuna cewa ana zaman dar-dar ganin yadda shugabannin jam’iyyun APC da PDP suke cece-kuce tare da zargin juna kan zaven.

Tuni manyan kungiyoyin kabilu suka raba sheka sakamakon mara wa Buhari da Atiku, lamarin da ake ganin ka iya kawo zagon kasa.

Kungiyar Afenifere ta Yarbawa da Ohaneze ta Ibo da Dattawan Arewa (NEF) da kuma ta Kare Muradun Arewa (ACF) duk sun rabu sakamakon ayyana goyon baya ga Atiku ko Buhari.

Da Aminiya ta tuntuvi wani masanin ilimin siyasa Aminu Dan Daura ya ce wannan ba sabon abu ba ne. “Abin tambaya  shi ne, shin su wadannan dattijan kabilu suna zave? Ko kana ganin za su iya canja akalar jama’arsu? Ban yi tsammanin za su iya bai wa Atiku ko Buhari mulki ba; domin yawancinsu zamaninsu ya wuce. ’Yan Najeriya ne kawai za su zavi wanda suke so,” inji shi.

Wata mai binciken al’amuran Afirka a Cibiyar Royal Institute of International Affairs, Chatham House a kasar Ingila, Dokta Lena Koni Hoffman, ta bayyana wa Aminiya cewa babban abin tsoro shi ne yadda Buhari ko Atiku za su yarda da sakamakon zaven da za a gudanar gobe.

“Yarda da faduwa a lokacin zave a Afirka babban al’amari ne kuma mai wuya. Muna fata dukansu za su yarda da zavin jama’a domin ci gaban kasarsu,” inji ta.

A shekaranjiya Laraba, Shugaba Buhari da Alhaji Atiku sun sake rattaba hannu a wata yarjejeniya a karkashin shugabancin Abdulsalami Abubakar, cewa za su yarda da sakamakon zave in har an gudanar da shi bisa gaskiya da adalci.

Shugaban Hukumar Zave ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a wata ganawa da ya yi da masu sa-ido kan harkar zave daga kasashen Rainon Ingila, a karkashin tsohon Shugaban Kasar Tanzaniya, Mista Jakaya Kikwete, ya yi alwashin cewa za su gudanar da zave mai inganci.

“Ai zamanin yin magudin zave ya wuce, yanzu akwai na’urori na zamani da babu yadda za a yi a raba kuri’a ta hanyar magudi. Haka kuma za a fadi yawan kuri’u da aka kada a take a kowane wajen zave bayan an kammala,” in ji shi.

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammad Abubakar Adamu, ya ce sun kammala shiri tsaf domin tabbatar da an yi zaven cikin lumana.