✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Najeriya za ta yi wasan karshe da Habasha

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasa zagaye na biyu da kasar…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasa zagaye na biyu da kasar Habasha a gasar neman gurbin zuwa cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.

Wasan zai gudana ne a garin Kalaba kuma ana sa ran daukacin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za su hallara don kashe kwarkwatar idanu.
A wasa zagaye na farko da ya gudana a watan jiya a kasar Habasha, Najeriya ce ta lallasa Habasha da ci 2-1 da hakan ta sa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles take bukatar akalla kunnen doki ne a wasan don ta haye gasar cin kofin duniya.
Sai dai ’yan wasan Habasha sun sha alwashin biyo Najeriya har gida don su yi mata lalata, ma’ana sun shigo da burin doke Najeriya a gida ne kamar yadda ita ma Najeriyar ta bi su har gida ta samu nasara a kansu.
Don haka wasa ne da zai yi zafi, duk kasar da ta yi sake aka samu nasara a kanta, to sai buzunta.
Tuni ’yan kwallon da Koci Stephen Keshi ya gayyato suka halarci sansanin horar da su. Su kuma ’yan Habasha sai a jiya Alhamis suka isa garin Kalaba a shirye-shiryensu na fafatawa a wasan.
Wasan zai gudana ne da misalin karfe hudu agogon Najeriya.