Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gobe Shugaba Buhari zai tafi Saudiyya

A gobe Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah da kuma amsa gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz ya yi masa a kasa mai tsarki.

Shugaba Buhari zai tafi Kasa mai tsarkin ne tare da wasu hadimansa na kusa, ana sa ran zai dawo ranar Talata 21 ga Mayu 2019, kamar yadda mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya sanar.

ADVERTISEMENT