✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a binne gawar mahaifin Aki

dan fim daga Kudancin Najeriya, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da lakanin ‘Aki’ zai yi bikin binne mahaifinsa a gobe Asabar.Mahaifin Aki, Mista Michael…

dan fim daga Kudancin Najeriya, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da lakanin ‘Aki’ zai yi bikin binne mahaifinsa a gobe Asabar.
Mahaifin Aki, Mista Michael Ogbonnaya Ikedieze ya mutu ne a ranar 18 ga watan jiya amma sai gobe ne za a yi shagalin binne shi, kamar yadda al’adarsu ta tanada, a garinsu, Uzuakli da ke Jihae Abia.
Kasancewar dan wasa Aki mai farin jinin jama’a, wanda kuma wasanninsa na barkwanci ke daukar hankalin ’yan kallo da yawa, ana sa ran halartar dinbin jama’a a bikin na binne mahaifinsa.
Cikin wadanda ake sa ran halartarsu, sun hada da hamshakan ’yan wasan fim na Najeriya da ’yan siyasa maza da mata da kuma sauran al’umma da ke da ruwa da tsaki da harkokinsa.