Da Dumi Dumi

Gobe za a dawo da ‘yan Najeriya 320 daga Afirka ta Kudu

Mahukuntan kamfanin jirgin saman Air Peace, sun bayyana cewa za a dawo rukuni na biyu na ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu a gobe Talata.

Ana saran saukar ‘yan Najeriya a jirgin saman na Air Peace da misalin karfe 7:00 na yamma a gobe.

Shugaban kamfanin Air Peace Allen Onyema, ya ce a tsakar daren yau jirgin zai bar najeriya ya sauka a Afirka ta Kudu da safe sannan ya bar kasar da rana ya sauka a jihar Legas.

Allen, ya ce a cikin ‘yan Najeriya 600 da suke shirin dawo wa Najeriya an tantance mutum 360 da zasu dawo.

ADVERTISEMENT
Share