✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Gobe za a shawota tsakanin Madrid da Madrid a Sifen

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar ne ake sa ran za a…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar ne ake sa ran za a kece raini a tsakanin kulob din Real Madrid da kuma na Atletico Madrid.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya a filin wasan Real Madrid wato Santiago Bernabeu.

Wannan wasa yana daga cikin wasa mafi zafi a gasar ta La-Liga, kuma kungiyoyin biyu sun fito ne daga gari daya, wato Madrid.

A duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu hankalin duniya kan karkata ne don ganin yadda wasan zai kaya, don haka wasan goben zai yi armashi.

Kawo yanzu kulob din FC Barcelona yake saman teburin gasar da maki 13 sai Real Madrid ita ma da maki 13 sai Albes mai maki 10 sai Celta bigo mai maki 8.

Yanzu dai hankalin masoya kwallon kwallo musamman magoya bayan kungiyoyin biyu sun zuba ido su ga yadda wasan zai kaya.

Allah Ya sa a kalla lafiya kuma a tashi lafiya a gidajen kallon kwallo musamman wadanda ke Arewacin kasar nan.