Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gobe Zakzaky da matarsa za su tafi Indiya

 

A karshen wannan mako ne wato ko gobe Asabar ko jibi Lahadi ake sa ran Jagoran Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ta mbaiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat za su tafi Indiya domin duba lafiyarsu bayan da kotu ta bayar da belinsu kan rashin lafiya.

ADVERTISEMENT

Zakzaky da matarsa suna shirin tafiya wani asibiti da ke garin Medanta a birnin New Delhi da ke kasar Indiya bayan Alkalin Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ya amsa bukatarsu a ranar Litinin da ta gabata tare da sharadin tafiya tare da Ma’aikatan Tsaro na Farin Kaya (DSS) a matsayin masu yi masa rakiya da kuma sa-ido.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarni ga Sheikh Zakzaky da matarsa su kasance a asibitin da aka amince da shi wato (Medanta Hospital) a Birnin New Delhi na kasar Indiya har tsawon lokacin da za su samu sauki daga rashin lafiyar tasu. Sannan su dawo Najeriya domin su ci gaba fuskantar shari’ar da ake yi musu.

ADVERTISEMENT

Hukumar DSS ta fitar da sanarwar ta bakin Kakakinta Dokta Peter Afunanya, inda ta tabbatar samun umarnin kotun, “Za mu yi aiki tare da masu ruwa-da-tsaki don ganin an bi umarnin kotun,” inji shi.

Tun farko Aminiya ta ruwaito yadda Kungiyar IMN ta rika zanga-zanga a Abuja, kafin wasu manyan mutane su sanya baki wajen ganin an samu maslaha.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Kaduna ta bukaci Babbar Kotun Jihar ta nemi a sanya “Wasu sharudda game da damar tafiya neman maganin” da kotun ta bayar ga Zakzaky da matarsa.

Ciki sharuddan akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta samu tabbaci daga Kasar Indiya cewa, “Ba za ta amince da bukatar neman mafaka ta kowace irin siga daga wajen mutanen biyu ko wani daga gefe ba.”

Sauran sharuddan kamar yadda sanarwar da Kwamishinan Al’amuran Cikin Gidan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu kuma BBC ya ruwaito, sun hada da:

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta tabbatar da Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat sun nemi ganin likita a Asibitin Medanta na Indiya, kuma su yi duk shirye-shiryen diflomasiyya tare da tsare-tsaren ganin mutanen biyu sun bi ka’idojin da aka kafa na tafiya neman lafiya.

Sai kowanensu ya yi alkawarin zai dawo Najeriya don ya ci gaba da fuskantar shari’a da zarar an sallame shi daga asibiti, kuma su ne da kansu za su biya wa kansu kudin tafiya da na magani da dawainiyarsu lokacin da suka je neman lafiyar.

Na hudu kowannensu ya gabatar da fitattun mutanen da aka aminta da su guda biyu don tsaya musu, kuma daya daga ciki ya kasance Sarki mai daraja ta daya a Najeriya da kuma wani fitaccen mutum da ke Kaduna wanda shi kuma zai yi alkawarin kawo su a duk lokacin da aka bukata. Kuma sai masu tsayawar sun gabatar da shaidar gida ko fuloti a cikin Kaduna.

Wadanda ake kara  kowannensu ya yi alkawari a rubuce kuma lauyansa ko nata sun sa hannu cewa, a lokacin da suke neman lafiya a Indiya ba za su yi wani abu na kawo cikas ga shari’ar da ake yi musu ba, ko kuma zaman lafiya da tsaron Najeriya da ma dokokin Indiya ta kowace irin siga.

Sannan jami’an tsaron Najeriya su yi wa Zakzaky da maidakinsa rakiya, kuma su kasance tare da su a tsawon lokacin da ake yi musu magani a Indiya ta yadda za su dawo da su bayan an sallame su daga asibiti.

Sharadi na bakwai shi ne Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Indiya sai ya  tantance mutum, kafin ya ba duk wani damar ziyartar mutanen da ake kararsu lokacin da suke Indiya.