Search
Subscribe
Godiya ga Ubangiji

Godiya ga Ubangiji

Ku yi godiya ga Ubangiji, gama Shi nagari ne, ƘaunarSa madawwamiya ce! 1 Tarihi 16:34”.

Ba abin da za mu iya ba Ubangiji Allah domin yawan alheranSa zuwa gare mu sai dai kalmar godiya.  Muna yi wa Ubangiji godiya domin yawan alheranSa zuwa gare mu, Ya kuma bar mu cikin masu rai har zuwa yau. Godiya ta tabbata ga Ubangiji kadai, ba da ikon kanmu ba, ko ilimi, kudi, basira da kariyar kanmu ba ne muka iya ganin yau, amma ikonSa ne kadai ya kawo mu wannan lokaci.

Babu shakka akwai tsananni cikin rayuwan dan Adam a wannan duniya, a nan cikin kasarmu ma muna ta fama a koyaushe, amma fa duk da haka sai mu lura Ubangiji bai bar mu hakan nan ba, akwai alheranSa da dama zuwa gare mu. Idan za mu iya tunawa baya daga farkon bana; kariyar da Ubangiji Ya ba ka kyauta, numfashi, abinci, biyan bukatu, lafiyar jiki,  wadansu za su ce ai bukatata a bana in gina gida, ko in yi aure, ko in sayi mota da makamantansu, amma wannan kan samu ne idan nufin Allah ne zuwa gare ka. Ubangiji Yakan bude mana hanya a lokacin da ya yi daidai da za mu ci moriyarsa ba tare da wata damuwa ko guna-guni ba; Irmiya 29:11 na cewa, “Gama na san irin shirin da Na yi muku, Ni Ubangiji Na fada. Shirin alheri, ba na mugunta ba…” Haka kuma ya kamata mu san cewa nufin Ubangiji zuwa gare mu daban yake da namu nufin cikin Littafin Ishaya 55:8-9, Ubangiji Ya ce, “TunaniNa ba kamar irin naku ba ne, Al’amuraNa kuma daban suke da naku. Kamar yadda sammai suke can nesa da kasa, Haka al’amuraNa da tunaniNa suke nesa da naku. Idan har rayuwarmu na bisa tafarkin Ubangiji ne, za mu iya ganin dalilai marasa kimantuwa da za mu yi wa Ubangiji godiya ba fasawa.

Za ka iya kirga alheran Ubangiji zuwa gare ka, iyalenka, ’yan uwa da masoya? Ka gwada ka gani. Idan har za ka iya, za ka ga cewa bukatunka ba su kai ko kwatar alheran da Ubangiji Ya yi maka ba. Wato mukan dauki damuwoyinmu da fadi ko kuma mu ce kusa-kusa da sukan hana mu ganin yawan alheran da Ubangiji ke yi mana a kullum. Misali, ka dauki kwandalar Naira daya idan za ka samu, ko kuwa mu ce tsabar masara ka rike kusa da idonka, idan ka kawo kusa da idanunka za ka ga cewa wannan tsabar ko kwandalar kan iya hana ka ganin fadin abin da ke gabanka ko sararin duniya, hakan nan yake idan muka dauki bukatunmu da damuwoyinmu kusa cikin rayuwarmu, ba za mu iya ganin girman alheran Ubangiji ba a rayuwarmu.

Domin haka, sai mu zama masu godiya a koyaushe; dare da rana ga Ubangiji don ba da ikon kanmu ba ne muke numfashi ko na sakan daya balle mu ce na tsawon shekara daya. Ubangiji Ya ba mu wannan kyauta ko sisi ba mu biya ba, sai ya zamanto godiya ne ta gagare mu da guna-guni? Ka yi tunani dai. Idan ka je asibiti yau za ka ga wadansu da ba sa iya numfashi da kansu sai da taimakon wasu na’urori, numfashin ma na cikin wani gwangwanin karfe, ka san nawa ake biya domin wannan na rana daya? Wadansu zuciyarsu ba ta iya bugawa sai da taimakon na’ura, amma ga ka nan kana ta shakar numfashi ba na shekara daya ba na tsawon shekarunka a duniya. Ba za mu iya biyan Ubangiji ba, rayuwarmu tana hanunSa, Ya kuma san duk abin da ke tafe cikin rayuwar kowane dan Adam. Idan har Mai iko duka na sane da bukatunka, me ya sa za ka girmama damuwarka fiye da yi wa Ubangiji godiya domin ikon sanin yanayin da kake ciki da kuma ikon magance su.

A lokuta da dama ba mu ba wa Ubangiji zarafi don Ya ziyarce mu a lokacin da muke cikin damuwa, mukan manta cewa Ubangiji Rayayye ne Yana kuma cike da ikon komai a sammai da duk fadin duniya, Shi kadai ne kuma zai magance mana matsalolinmu. Abin da Yake bukata gare mu  shi ne godiya. Bari rayuwarmu ta zama cike da godiya ga Ubangiji. Mu gode maSa mu kuma dogara ga ikonSa ba ikon kanmu ba, ta wurin yin haka ne za mu iya sanin yawan alheranSa zuwa gare mu.

Filibiyawa 4:6-7, “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsayar da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.”

Bari Ubangiji Ya albarkace mu, amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin