✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gonin Gora: Zuwan baki ya mayar da garin kadarkon mutuwa – ’Yan Asalin Garin

Gonin Gora gari ne da ke a cikin Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna. Garin na a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ne kuma mazauna…

Gonin Gora gari ne da ke a cikin Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna. Garin na a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ne kuma mazauna garin a shekarun baya da suka wuce, yawancinsu ’yan kabilar Gbagi daý Hausawa da Fulani ne.

A cewar mazauna garin na Gonin Gora, an kafa shi kusan shekara dari biyu da suka wuce kuma Gwarawan da ke yankin sun fito ne daga yankin Borno da ke Gabashin Arewacin kasar nan.

A wancen zamani gari ne da al’ummarta ke zaune lafiya ba tare da nuna bambancin addini ko na kabilanci ba. A yanzu haka  a Gonin Gora akwai kabilu daban-daban da ke zaune a cikinsa kamar Gbagi da ke Sarauta da Katafawa da Ibo da Igala da Idoma da Yarabawa, kuma akasarinsu. Ta fuskar addini, yawancinsu mabiya addin Kirista ne, kodayake a can baya akwai al’ummar Fulani Musulmi a garin, amma saboda fitintinu masu nasaba da kabilanci da addini sai suka yi kaura daga garin a shekarun baya.

A shekaru kusan 18 da suka gabata, Gonin Gora ya yi kaurin suna, musamman saboda rawar da ake zargin matasan yankin ke takawa wajen tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a duk lokacin aka samu hargitsi a jihar. Sai dai wasu mazauna yankin na musanta zargin da ake wa matasan nasu na tare titi, wanda hakan ya yi sanadin rasa rayukan matafiya masu yawa a sakamakon kashe su da aka yi.

A cewar wasu mazauna garin na asali, tsirarun ’ya’yan wasu kabilu baki ne ke aikata laifin, ba ’yan asalin ’yan garin nasu ba.

Aminiya ta fahimci cewa Gonin Gora da aka sani da zaman lafiya ya yi kaurin suna ne saboda al’ummar kabilun Kataf da Kaje da Idoma da Ibo da saurnansu da suka baro wasu unguwanni kamar Rigasa da Kawo da Rigachikun da sauransu a lokacin da aka yi rikici kan Shari’a a shekarar 2000.

Sakamakon yawan tare titi da ake zargin matasan na Gonin Gora da yi ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa’i ýya sha alwashin tayar da mutanen wannan yanki muddin matasansu suka ci gaba da halaka mutane a kowani lokaci. A cewar gwamnan, bai ga dalili da zai sa wasu mutane za su rika tare kan hanya suna kashe mutane ba.

Sai dai kalaman na Gwamna Nasir El-rufa’i ya janyo cece-kuce a ciki da wajen jihar a yayin da wasu ke ganin bai kamata ya fadi haka, ba kasantuwar wai a wasu unguwannin ma matasan suna tare titi lokacin rikici.

Aminiya ta samu damar jin tabakin Sarkin Yakin Gonin Gora, Simon Bawa Bije wanda kakansa ne mai gari Bije, wanda ýya fara zama a garin tun a lokacin da babu hanya sai an tsallake rafi ake zuwa garin. A cewarsa, Gonin Gora na daya daga cikin tsofaffin garuruwa da ke a nan Kaduna.

Ya ce tarihi ya nuna cewa ainihin mazauna yankin sun fito ne daga yankin Borno, kafin suka fara zama a Karamar Hukumar Igabi, daga nan wasu daga cikinsu suka zauna a Doka, wasu kuma suka zauna a Kurmin Gwari, wasu a Kakau wasu kuma a Gonin Gora. Kuma dukkansu ’yan Kabilar Gbagi ne. Ya ce a lokacin daga Hausawa sai Gbagi da kuma Fulani ke zaune a Gonin Gora.

“Rikicin da aka yi shekarun baya ya sa mafi yawancin Gwarawa da sauran kabilu da suka taso suka bar can suka dawo Gonin Gora. Kuma marigayi tsohon Sarkin Gonin Gora ne ya ba su filaye suka yi gini kyauta suka zauna, musamman yan kabilar Gbagi.

“Wasu daga Kawo da Rigachikun suka gudo suka dawo Gonin Gora amma a shekarun baya ana kiran wajen ne da sunan Unguwar Bije watau Bije din shi ne kakana. Shi ne Sarkin garin a lokacin.

“A lokacin kuruciyata, da ’ya’yan Hausawa da Fulani muka girma a Gonin Gora. Wadannan kabilu kawai na sani baya ga kabilata ta Gbagi. A lokacin muna zaune lafiya babu bambanci.”

Game da sabanin addini da ya kunno kai a yankin sai ya ce, “shigowar wasu kabilu cikinmu ýne ya kawo hakan. Yaruka sun shigo kuma sai batun addini ya zo ya raba kawunanmu. Wannan shi ne gaskiyar zancen amma ni kam na girma ne tare da Musulmi. Da wuya ka iya bambanta Bahaushe da dan kabilar Gbagi a zamanin. Amma zuwan Boko ne ko kuma zan ce ilimi ne ya kara raba kawunanmu.”

A kan yadda yake ji idan ana danganta Gonin Gora da tashin hankali sai ya ce: “Rashin sani ne ya sa, ai babu yadda za ka yi ka ce gari baki daya su ke tare hanya. A yankin Gonin Gora an yi lokacin da Musulmi suka yi sarauta a yankin. Wannan ya sa nake ganin muna yaudarar kawunanmu ne kawai, mu ce wai ba za mu rayu da juna ba. Ni din nan na zauna da Musulmi, domin har shugabacin riko na yi na Karamar Hukumar Giwa da kuma Igabi a jihar nan tamu.

“Don haka ina da mu’amala mai kyau da Musulmi da ke yankin. Suna kirana ina kuma ziyartarsu, sun sani babu ruwana da duk wani abu da za ka nuna bambancin addini ko kabilanci. Abin da kawai na sani shi ne dukkanmu ’yan Adam ne.”

Da Aminiya ta so jin ko su waye ke tare titi da ake zargi a Gonin Gora, sai ya ce: “Yanzu abu ne mai wuya ka iya bambanta masu wannan abu, domin akwai shaye-shaye da ya bata matasa.

“Mu abin da muke cewa a kullum shi ne, a fito a kama duk wanda ke tare hanya a lokacin rikici. Abu ne mai wuya a ce wai ana tare hanya saboda kar ka manta fa babban titi ne. Wannan titi da ake Magana, yinsa a garin fa mu alheri ne domin a da sai dai a bi ta Birnin Gwari ko mu bi ta Keffi zuwa Abuja. Saboda haka a kullum abin da muke cewa shi ne, duk wanda aka kama da tare hanya sai a hukunta shi.

“Kuma ai ko a wannan lokaci da aka yi hatsaniya ai babu wanda ya tsare hanyar. Gwamna ne kawai ke dawowa daga Abuja ya zo ya tarar da jama’a na tsoron wucewa. Da ya tambaya sai aka ce masa wai an tsare titi, shi kuma sai ya wuce gaba mutane suka bi shi. “Da suka bi shi sai suka lura babu wanda ya tsare hanya. Ai babu wanda ya isa ya tare babban titi irin wannan a yanzu.”

Da yake mayar da martani ga jawabin Gwamna cewa idan har aka sake tsare titin Gonin Gora zai tada garin, sai Simon Bawa ya ce: “Idan har tsarin damokuradiyya ake bi, gwamnan ba shi da hurumin yin hakan. Ba karamin gari ba ne da za ka ce za ka tashi mutane lokaci daya. Kai ba ma zai iya yi ba, ya dai fadi ne kawai. Sai dai idan ba mulkin damokuradiyya ake yi ba. Mu ba mu ki cewa duk wanda aka samu da hannu a hukunta shi ba.”

Ya kuma yi kira ga jama’a cewa abin da mutum bai gani ba, to kada ya yi magana a kansa. Abin da ya gani da idonsa sai ya yi magana a kansa. “Sannan kuma akwai bukatar mu zauna lafiya da junanmu domin, zama lafiya ya fi zama dan sarki. Dukkanmu ’yan Adam ne da ke neman yardar Allah. Babu wanda ya taba zuwa ya ga yadda Aljanna take amma duk muna son mu shiga,” inji shi.

Alhaji Tajudden Ajibagde, daya ne daga cikin mazauna garin na Gonin Gora kafin aka kona masa gida lokacin rikicin Sarauniyar Kyau da aka yi a jihar a shekarar 2000. Ya ce ya fara zama a garin ne a shekarar 1990, bayan ya kammala gininsa a shekarar 1989 a Hayin Kataf.

“A lokacin akwai Musulmi da wadanda ba Musulmi ba a garin amma a Hayin Kataf din ni kadai ne Musulmi. Idan na tuna abin da ya faru sai in ji kamar in yi kuka. A lokacin da aka yi zanga-zanga na bikin sarauniyar kyau na duniya wanda jaridar Thisday ta janyo mana.

“Lamarin ya faru ne a watan Nuwamba 28 na shekarar 2000, muna cikin azumin Ramadan. Ina zaune tare da iyalina aka ce ana zanga-zanga cikin gari. Can sai na hango gungun mutane sun nufo inda muke kuma kafin ka ce me sai suka kona wani masallaci da ke kusa da gidana, daga nan kuma sai gidana. “Kawai sai na ji an soma jifan gidana amma sai wasu daga cikinsu suka ce ba za su bari a taba ni ba. Amma daga baya sai muka bar gidan. Na fita na je neman yarana uku a lokacin amma wani Kirista dan kabilar Tibi ya dauke su, ya ajiye mini su a gidansa. Ni ma a wajensa na kwana,” a cewarsa.

Game da tare hanya sai ya ce, “Gaskiya a iya sanina babu matasan Gonin Gora da yawa cikin masu aikata hakan, musamman Gbagi. Ban ce babu su ba amma dai ba su da yawa.

‘Na san lokacin da aka kashe wani Honorabul Bala a wannan hanya, domin ana rikici sai ya fito da nufin yin magana amma sai suka kashe shi. Wanda hakan ya sa marigayi tsohon Mataimakin Gwamna Steben Shekari ya so ya tayar da Gonin Gora amma aka yi masa magana ya bari.

“Masu wannan gari Gbagi ne, ba su neman fitina saboda haka akwai bukatar a gano masu tare wannan hanya. Akwai bakin mutane da suka dawo daga wasu wurare da aka bai wa filaye a wajen domin su zauna.

Suna daga cikin masu tada fitina a wannan gari. An san wadanda suke tare hanyar, idan ban manta ba, marigayi Sarki Yusuf Doma a garin sun nemi su gyara mini gidana da aka kona domin in sake komawa amma na fada masu cewa ni ba zan koma ba, dole sai an gano yaran da ke tayar da fitina a garin.”

Daga karshe, ya ba da shawarar cewa: “Wannan batu na rabuwar unguwannin Musulmi da Kirista ba alheri ba ne. Dole ne Musulmi da Kirista su zauna tare da junansu, domin ci gaban jama’a.”