✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudunmuwar Zuri’ar Matawallen Katsina ga kasa

Tarihi shi ne babban alkali game da gudunmuwar zuri’a Matawallen Katsina Alhaji Musa ’Yar’aduwa, tsohon minista, kuma mahaifin Mataimakin Shugaban kasa a mulkin soja, da…

Tarihi shi ne babban alkali game da gudunmuwar zuri’a Matawallen Katsina Alhaji Musa ’Yar’aduwa, tsohon minista, kuma mahaifin Mataimakin Shugaban kasa a mulkin soja, da kuma Shugaban kasa na zamanin farar hula. Alhaji Shehu Musa ’Yar’aduwa, shi ya gaji sarautar Matawalle. Don haka tarihi ba zai manta da shi ba, a Jiharsa ta Katsina da ma kasa baki daya.
An haifi Marigayi Alhaji Shehu Musa ‘yar Aduwa a ranar 5 ga watan Maris na Shekarar 1943, shi ne wa ga Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, tsohon shugaban kasar nan, kuma shi ne mahaifin Murtala ‘Yar’aduwa, tsohon ministan tsaron Nijeriya.
Mahaifinsa, Marigayi Alhaji Musa ‘Yar adua, Matawallen Katsina, ya kasance tsohon malamin makaranta, Bafullatani, mutum mai amana, wanda ya taba zama Ministan Babban birnin Tarayyar a Jamhuriya ta farko (a lokacin fadar gwamnati na Legas) na tsawon shekaru tara, watau daga shekara ta 1957 izuwa 1966.
Marigayi Shehu Musa ‘Yar adua, ya yi aji guda da Shugaba Muhammadu Buhari a makarantar Katsina Probincial School, wadda yanzu ake kira da Gobernment College Katsina, a nan ne ya samu nasarar cinye jarrabawar daukar sojoji, inda aka dauke shi a matsayin soja a wancan lokaci, tare da su Buhari da wasu manyan mutane a kasar nan a wajen shekarar 1962. Daga baya aka ce saboda kwazon da ya nuna, aka tura shi karo karatu a Ingila, can wata makaranta mai suna ‘Royal Military Academy’.
A shekarar 1964, Marigayi Shehu ‘Yaradua ya dawo Najeriya daga kasar Birtaniya yana da mukamin ‘2nd lieutenant,’ inda aka tura shi Inugu aiki a karkashin shugabancin Kanar Adekunle Fajuyi. An ce a lokacin yakin basasa, Shehu ‘Yar aduwa ya zamo kwamandan wata bataliya, wadda take aiki bisa umarnin Marigayi Janar Murtala Muhammad. Shi ne har wani labari ya zo cewa Shehun ya taba jagorantar wani harin sunkuru ga sojojin Biyafura don karbe ikon Onicha, wadda a lokacin sojojin Biyafurar suka mamaye. Amma cikin rashin sa’a, sai sojojin Biyafuran suka yi luguden wuta a kan wannan runduna, ciki kuwa har da marigayi Shehu ‘Yar’aduwa domin yana ciki. Wannan abu ya yi sanadiyar mutuwar daukacin wadannan dakaru, kalilan ne suka sha da kyar, ciki har da Jagoranta Shehu ’Yar’aduwa.
Bayan an kammala yakin basasa, Janar Murtala ya karbi ragamar shugabancin kasa a shekarar 1976, sai ya nada Shehu Yar’aduwa a matsayin ministan zirga-zirga. Wanda kuma aka dora wa alhakin rage cunkoso a tashar jiragen ruwa da ke Legas. A wannan lokacin ne gwamnati ta yi wani yunkuri na ba da kwangilar suminti, har ton miliyan 60 wanda za a yi amfani da shi don gina barikokin soja a fadin kasar nan. Sai dai daga baya gwamnati taga cewa babu isasshen wurin da za a ajiye sumintin a gabar tekun, shi ne aka yi shawarar rarraba kayan izuwa sauran tashoshin ruwa da ake da su, in ya so sai a kara gina sabuwar tashar jirgi a Legas. Kafin wadannan ayyuka su tabbata Allah ya yi wa Janar Murtala rasuwa.
Da hawan Janar Obasanjo kan karagar mulki kuma, sai aka canza wa Shehu Yar’aduwa wurin aiki, inda aka kara masa mukami zuwa shugaban ma’aikata, aka kuma dora wa ofishinsa alhakin samar da abinci wadatacce a wani shiri da aka kirkiro mai taken ‘Operation Feed the Nation OFN’.
Babban abin da Shehu Yar’aduwa ya dukufa da yi a lokacin, shi ne, samar da wadataccen takin zamani ga manoman Najeriya, tare da irin shuka ingattacce. A lokacin sa ne aka sawo kayayyakin noma na zamani, wadanda suka hada da motoci da injina da sauran na’urori, aka rarraba su lungu da sako na kasar, sannan aka dora alhakin koyar da hanyoyin amfani da su ga manoma a hannun matasa masu bautar kasa. Wannan abu ya yi sanadiyyar kara dankon zumunci a tsakanin matasan sassan kasar nan da kuma manoma na wancan lokaci, sannan ya cusa sha’awar yin noman a zukatan ‘yan kasa.
Daga baya, Shehu Yaradua ya jagoranci harkoki gami da tsare-tsare na ganin an ciyar da talaka gaba a lokacin mulkin farko na Shugaba Obasanjo. A lokacin sa ne aka kirkiro kananan hukumomi, aka kuma yi musu tsari wanda kai tsaye zai rinka taba talakan da ke kasa. Wannan tsari kuwa har yau ana cin moriyar sa, Domin masana sun tabbatar da cewa gwamnatin karamar hukuma ta fi kusanci da talaka fiye da kowacce gwamnati a kasar nan.
Baya ga haka, ya taimaka matuka a lokacin mulkinsu, don ganin an gudanar da zabe na farko a Najeriya. Domin kuwa a shekarar 1979, gwamnatin soja da su Shehu ’Yar’aduwa ke jagoranta a karkashin Janar Obasanjo suka mika mulki a hannun farar hula karo na biyu, a karkashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari bayan an gudanar da zabe. Don haka tunda an yi zabe, kuma an danka wa farar hula mulki, sai Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa ya ajiye kaki, ya koma gida a inda ya fara gudanar da kasuwanci. Amma tafiya ba ta yi nisa ba, sai kuma ya sanya rigar siyasa a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, kasancewar sa mutum ne mai son ganin komai ya tafi daidai a wannan kasa.
A lokacin ne Marigayi Shehu ’Yar’adua ya zama dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina, sannan da shi da Alhaji Ibrahim Dasuki, da wasu manya suka kafa kungiyar siyasa mai suna ‘Consensus/Democrat Group’ a shekara ta 1987. Kodayake daga baya kungiyar ta rushe inda aka mayar da makwafinta da wata babbar kungiya mai suna ‘Peoples Front’. Mambobin wannan kungiya su ne;- Babagana Kingibe da Abdullahi Aliyu Sumaila da Ahmad Rufa’i da Yahaya Kwande da Ango Abdullahi da Sabo Bakin zuwo da Babalola Borishade da Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Abdul’aziz Faruk. Wannan kungiya tana cikin jam’iyyar SDP, jam’iyyar da ta samu nasarar lashe kujeru masu rinjaye na zaben ‘yan majalisu da aka gudanar fiye da jam’iyyar NRC.
Marigayi Shehu ’Yar’aduwa ya yi futikar wanzar da mulkin dimokuradiyya na adalci a kasa, ya kuma ci karo da cikas iri-iri. Hakika abubuwa marasa dadi sun auku, wadanda ba su da alfanu, amma dai daga karshe an daure Marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa tare da Janar Obasanjo a gidan kurkuku na kiri-kiri, a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, har na tsawon shekaru hudu, inda a karshe Allah ya karbi ransa ranar 8 ga watan Disambar shekarar 1997. Allah ya jikansa.
Hakika, za a jima ana tunawa da Marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa saboda jajircewarsa gami da yin yaki domin kare hakkin talaka. Ya sadaukar da rayuwar sa a lokacin yakin basasa don ganin Najeriya ta zamo kasa daya dunkulalla. Ya kirkiro hanyoyin da gwamnati za ta rinka tallafa wa talakawan ta. Ya yi fada da tsoffin abokan sa sojoji a lokocin da ya yi ritaya, don ganin mulkin siyasa ya dore a wannan kasa. Shi ne kuma shugaban kwamitin gina Babban Masallacin kasa da ke Abuja har lokacin mutuwarsa. An ce sakon sa na karshe daga kurkuku ya fito ne a shekarar 1995, inda yake cewa “Kada ku damu sosai da ni, wannan abu sadaukarwa ce da ya kamata wasun mu su yi domin ‘yantar da kasar mu..”
Allah ya jikansa. Allah ya gafarta masa. Allah ya kyautata namu zuwan. Amin.
Gwarzo ya rubuto makalarsa daga Jihar Kano. 08060869978.