✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwa ta yi mummunan ta’adi a kasar Amurka

A ranar Lahadin da ta gabata, al’umma a Jihar Illinois ta kasar Amurka sun gamu da bala’in guguwa, wacce ta yi mummunar barna a sassan…

Yadda guguwa ta barnata sassan Jihar Illinois ta AmurkaA ranar Lahadin da ta gabata, al’umma a Jihar Illinois ta kasar Amurka sun gamu da bala’in guguwa, wacce ta yi mummunar barna a sassan jihar daban-daban.
Guguwar, wacce ta share gidaje da sauran gine-gine a Kudancin Illinois, ta kashe mutane takwas nan take.
Ya zuwa Talata kuwa, Hukumar Kula Da Yanayi ta Amurka ta tabbatar da mutuwar mutane 16 a Illinois da Arewa-Maso Yamma na Indiana.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Reuters ta ruwaito, ya zuwa Talatar da ta gabata, hukumomi sun kyale mutane zuwa kufan gidajensu domin laluben kayayyakinsu da suka yi saura.
“Muna bukatar mu bar mutane da yawa su shiga birnin, domin su lalabo wasu abubuwansu masu kima da suka saura, wadanda guguwar ba ta lalata ba.” Inji Gary Manier.
A Washington, akalla mutane 2000 ne gidajensu suka ruguje ya zuwa Talatar da ta gabata. Kamar yadda Mista Manier ya bayyana, ya ce shi da kansa ya kiyasta cewa gidaje 1000 ne suka ruguje a sakamakon guguwar da ta afku a Lahadin da ta gabata.
Masana sun bayyana cewa wannan guguwa ita ce irinta ta biyu mafi muni a tarihin kasar. Kamfanonin inshora dai suna ta tantancewa da harhada bayanai, domin gano kimar hakikanin barnar da guguwar ta haifar.
“Wannan guguwar ta yi muni sosai.” Inji Martin Petit, wani malamin kimiyya mai ritaya, wanda yake zaune kusan shekaru bakwai da suka gabata. Ya samu mafaka ne a kasan gidansa, shi da matarsa, a yayin da rufin gidansa na saman kasa ya kware. Haka suka zauna ba tare da wutar lantarki ba, tun daga faruwar guguwar a Lahadi.