Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Guguwar Fani ta kashe mutum 34 a Indiya

Akalla mutum 34 aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon guguwar Fani da ke gudun kilomita 180 a awa daya da ta kunno kai a yankin Puri na Jihar Orissa da ke kasar Indiya.

Sanarwar da aka fitar daga Ofishin Bayar da Agajin Gaggawa na jihar ta ce, a fadin jihar mtum 34 sun mutu inda 21 suka fito daga yankin Puri.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce, yankin Puri ne ya fi illatuwa da guguwar inda sama da cibiyoyin kula da lafiya dubu daya da makarantu sama da dubu biyar suka samu matsala.

Guguwar ta shafi mutum dubu 14 da 835 inda dabbobi dubu 17 da 280 suka mutu.

ADVERTISEMENT

Firayi Ministan Jihar Orissa Nabeen Patnaik ya ce za su bayar da taimakon kudi da shinkafa ga jama’ar da lamarin ya shafa.

Patnaik ya kara da cewa dubban mutane sun rasa ruwan sha da  wutar lantarki sakamakon guguwar, kuma gwamnatinsu ta bayar da taimakon abinci kyauta na kwana 15 ga wadanda lamarin ya rutsa da su.