✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gurgun yaro ya samu keken guragu uku

Wani yaro gurgu dan shekara tara mai suna Jibrilla Bello ya samu kyautar keken guragu uku. Jibrilla Bello dai shi ne wanda jaridar Daily Trust…

Wani yaro gurgu dan shekara tara mai suna Jibrilla Bello ya samu kyautar keken guragu uku.

Jibrilla Bello dai shi ne wanda jaridar Daily Trust ta buga labarinsa a makon jiya cewa yana neman taimakon keken guragu saboda wanda yake amfani da shi ya lalace.

Kwana daya kacal da fitowar labarin sai jama’a da kungiyoyi suka nuna niyyarsu ta taimaka wa yaron wanda maraya ne.

Cikin wadanda suka bayar da taimakon keken guragun akwai wata mata da ke zaune a Abuja  da ba ta so a ambaci sunanta da ta sayi sabon keken guragun a kan  Naira dubu 40 ta ba Jibrilla.

Matar ta ce za ta kara taimaka wa Jibrilla ta wata hanya da ba ta bayyana ba.

Sai kuma Bankin Zenith wanda jami’anta suka kai wa Jibrilla keken guragu har gida a can garin Sunkani da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola a Jihar Taraba.

Sai kuma wani mazaunin Ikko a Taraba mai suna Malam Muhammed Garba wanda ya saya masa guda daya, ya tura Jalinngo inda daga can za a kai wa Jibrilla Bello a Sunkani.

Kakan gurgun Malam Suleiman Adamu ya gode wa wadanda suka taimaka wa Jibrilla.

Ya ce Jibrilla maraya ne shi kuma ba ya da karfin saya masa keken guragu, sannan ya kara da cewa zai sa Jibrilla a makarantar firamare domin yaron yana son shiga makarantar boko.