✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwagwarmayar da na sha kafin in zama Zakaran Musabaka ta Duniya – Hafiz Idris

Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana Idris Abubakar Muhammad. An haife ni a garin Kirinuwa a Karamar Hukumar Marte a Jihar Borno a 1999, wato shekarata…

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Idris Abubakar Muhammad. An haife ni a garin Kirinuwa a Karamar Hukumar Marte a Jihar Borno a 1999, wato shekarata 20 ke nan. Bayan da na shekara 6 mahaifina ya zo da ni  nan garin Maduguri don koyon karatun Alkur’ani, a Tsangayar Sheikh Goni Idris Anna’if, to a tsangayar akwai wani kanen mahaifina, a wajensa na fara karatu na yi wasu shekaru a wajensa. To bayan nan sai na ci gaba da karatuna a wajen wadansu manyan malamai, irin su Sheikh Goni Usman Goni Idris Limamin Juma’a ne da Idi a Masallacin Sheikh Goni Idris da ke Unguwar Mashimari, har na haddace Alkur’ani.

Wane kalubale ka fuskanta lokacin da baro gida domin neman ilimi?

To gaskiya kalubalen da na fuskanta a farko shi ne idan yaro yana karami abin ba sauki, da yake lokacin mutum bai san abin da iyayensa ke hangowa ba, mutum zai ga kamar iyaye ba sa sonsa ne, ashe ba haka abin yake ba. Akwai daliban da muke tare da su a wajen karatun, bayan mako guda ko biyu suna zuwa ziyarar iyayensu ko ’yan uwansu, amma ni sai Malam ya hana ni sai bayan shekara biyu, haka nake zuwa ziyarar iyayena a can kauye, ko an yi hutun shekara sauran za su tafi hutu amma ni sai dai in sun dawo su ba ni labarin gida, amma ni sai bayan shekara biyu, to wannan ne kalubalen da na fuskanta a farko.

Ka taba shiga makarantar boko?

Na yi karatun boko amma ban yi nisa ba, don ban ma kammala sakandare ba

Da hadda da tilawa da tajwidi ya dauke ka shekara nawa?

Zan iya cewa duk sun dauke ni kamar tsawon shekara biyar.

Ga shi ka zama Zakaran Musabaka ta Duniya ta bana, yaya ka fara?

Na fara shiga musabaka ce a shekarar 2017, to dama idan mutum zai fara musabaka sai ya samu kwararrun malaman da za su koya masa karatun musabaka wato karatu da tajiwidi da kuma sautin da ka farawa da shi kuma da shi za ka karasa. Kuma na fara koyo a gida da makaranta kafin mu je karamar hukuma, na kuma koye su a wajen malamaina irin su Sheikh Goni Usman da Sheikh Goni Dahir, da Goni Idris Anna’im, na kuma fara ne da matakin Karamar Hukumarmu ta Jere a Jere (B) na kuma fara da matakin Izu 40, da na samu nasara sai na wakilci Karamar Hukumar Jere a matakin jiha, da na sake samun nasara sai na wakilci Jiahar Borno, a matakin kasa, wanda na yi haka har sau biyu aka gudanar a jihohin Kwara da Katsina, a shekara ta 2017 da 2018. To bayan nan sai malamaina suka ce Izu 40 din ya isa tunda har na je sau biyu, sai suka ce mini zan yi Izu 60, to a lokacin gaskiya na ga kamar ba zan iya ba, domin na ga nauyin abin, ganin cewa akwai dalibai wadanda suka fi ni kwazo kuma sun dade a matakin. Amma sai suka kara min kwarin gwiwa suka ce ba komai zan iya. To sai na fada kai-tsaye na kuma bi umarninsu na fara musabakar Izu 60 daga matakin Karamar Hukumar Jere (B) har na samu nasarar zuwa matakin kasa da duniya wakilci Najeriya ke nan. Allah cikin ikonSa kuma Ya ba mu nasara amma kafin mu je na sun kara mana ilimomi da dama irin na karatun musabaka ba dare ba rana, musamman shi malaminmu Goni Dahir din ba ya gazawa. Komai aikin da yake yi kuma ko’ina zai fita tare muke fita da shi a mota domin ya ga cewa na iya. Da muka dumfari musabakar duniya a kasar Saudiyya shi ma Malam Goni Dahir din ne ya raka ni har can, to a can ma bai bar ni ba.

Alaramma Idris Abubakar Muhammad yana amsa tambayoyin manema labarai
Alaramma Idris Abubakar Muhammad yana amsa tambayoyin manema labarai

Da aka bayyana kai ne ka yi nasara yaya ka ji?

Ai murnar da na yi da gami da godiyar da na yi wa Allah abin ba ya misaltuwa, don ba farin cikin da ya fi wannan. A duniya a kuma cikin kasashe 103, a ce kai ne ka zama zakara, babu farin cikin da ya wuce wannan. Kuma ka san ni kadai ne na wakilci Najeriya duk da cewa kowace kasa mutum biyu ne suke wakiltarta.

Wane kira za ka yi ga ’yan uwanka matasa da suke neman ilimi irin naka?

Su jajirce su bi iyaye da malamai. In Allah Ya so za su samu abin da suke bukata. Ina kuma gode wa Gwamnan Jihar Borno  Farfesa Babagana Umara Zulum da ya ba ni kyautar mota da tsabar kudi har Naira miliyan biyra. Kuma ina gode wa tsohon Gwamna Sanata Kashim Shettima da ya bai wa iyayena gida da fili. Haka kuma ina gode wa Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai, saboda taimakawa da yake mana tare da goyon bayan da yake ba mu. Kuma ina mika godiyata ga daukacin malamaina da suka jajirce wajen koyar da ni tare da ganin cewa na samu nasara, Allah Ya saka musu da alheri da kuma gidan Aljanna.