✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwagwarmayar rayuwa: Waiwaye adon tafiya (4)

A cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ƙarfafa wa mata gwiwa tare da tallafa musu domin su iya dogaro da kansu, aka shirya wata…

A cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ƙarfafa wa mata gwiwa tare da tallafa musu domin su iya dogaro da kansu, aka shirya wata kasuwar baje kolin sana’o’in mata a filin wasa na Muhammadu Dikko. A wannan rana muka ga abin da ya ba mu mamaki. Mai girma Gwamna yana tsakiyar jawabi sai wata mata daga cikin taron jama’a ta ce tana da magana. Har an fara kwabar ta, sai kawai ya ce “A ba ta abin magana ta faɗi abin da ke ranta, ai da ƙuri’unsu muka zo nan.” Da ta gama nata jawabin, take ya haɗa ta da Kwamishinar Harkokin Mata domin a yi mata abin da ta nema. Ire-iren waɗannan akwai su da dama. Mutum ba zai gane wane ne Dallatu ba sai Allah Ya sa ya zo kusa da shi, amma ko da ba ka zo kusan ba, idan kana bibiyar tsarin da ya ɗauko na gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma, kai-tsaye za ka san ba abin da ke gabansa shi ne yadda zai kyautata wa al’umma. Shi ya sa babu wani lokaci da ya ware don yi ko duba aiki – koyaushe lokacin aiki ne a wurinsa. Tsakar dare, lokacin da mafi yawan mutane suke barci, sai ka ga ya fita duba aikin da gwamnati ta bayar, domin kawai ya tabbatar ana yin abin da ya kamata.

Alhaji Aminu Masari mutum ne da kafin ka samu mai haƙurin zama da mutane kamarsa sai an yi da gaske, ga haƙuri da natsuwar sauraron bayani; idan ana yi ba ya ƙosawa. Idan ka zo masa da magana ko buƙata, ba zai taɓa gaya maka abin da za ka ji daɗi ba, zai gaya maka abin da yake daidai ne kuma mai yiwuwa. Shi ya sa yake yawan cewa shi fa bai iya irin wannan siyasar ba, ta faɗi ko ɗaukar abin da ba zai yiwu ba daga baya a zo ana ’yar-ɓuya.

Idan kuma ya hada da aiki, to zai ba ka duk damar da kake buƙata domin ka samu nasarara. Kuma zai gaya maka shi fa har ga Allah ya fita, sai ka yi ƙoƙarin fitar da kanka ta hanyar kamanta gaskiya da sanin ya kamata. Kuma ka sani, yadda ka hau haka wata rana za ka sauka, don kafin kai, wadansu sun hau yau suna ina?

Akwai ranar da yake ce mana: “Na fi kowa son ganin na samu nasarar sauke wannan nauyin da yake kaina, domin kamar kasada ce na ɗauko, lokacin da na sauka daga kujerar ‘Speaker’ duk kasar nan, kowa na jinjina mini, to yanzu idan na kasa kai bantena a kan kujerar Gwamnan Jihar Katsina, ina kuma zan je in gyara kaina?”

Wannan shi ne ainihin yadda yake kallon nauyin da yake kansa, duk kuma wanda ke da irin wannan tunanin to kuwa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin nasara ta samu.

Abubuwa da dama mun samu nasarar aiwatar da su ko samar da su ta hanyar wannan aiki, amma waɗanda na fi alfahari da su, ba kamar na gyaran makarantu da aka yi, sai waɗanda cikin ikon Allah na zama silar samun aikinsu, a ciki akwai wanda har yau ban taɓa ganinsa ba.

Tun daga ranar 13 ga Janairun shekarar 2016 da na fara wannan aiki zuwa yau, ban taɓa ɗaukar matsala tawa ta ƙashin kaina, na kai wa Mai girma Gwamna ba, sai dai ta al’umma. Duk abubuwan da yake yi mini, yana yi mini ne a cikin karamci da ƙauna.

Tun da Allah Ya sa na fara hidimar Dallatu, sai na riƙe tarayyarmu da shi a matsayin amana. Yanzu ba Gwamna kawai nake kallonsa ba, ina kallonsa kuma na ɗauke shi a matsayin uba, domin bai riƙe ni da wasa ba, shi ma ɗa ya ɗauke ni.

Abokan aiki, abokan gwagwarmaya da kuma ’yan uwanmu da Allah Ya ƙaddara su cikin ɓangaren adawa, duk ina yi wa kowa fatan alheri tare da neman yafiya ga duk wanda na yi wa ba daidai ba, walau ta rashin sani ko kuma ajizanci irin nawa. Ina roƙon Allah Ya yafe mana baki ɗaya.

Wannan shi ne abin da Allah Ya ba ni ikon rubutawa a kan Dallatu da alaƙa ko hulɗata da shi, duk da cewa daga baya Allah Ya haɗa mu.

Ya Allah ina roƙon kariyarKa a kanmu baki ɗaya daga dukan sharri. Ya Allah kada Ka ba ni ikon kai masa (Dallatu) ƙarya, Ka ɗora ni kan kai masa gaskiya a koyaushe.