✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Amosun ya shiryawa barin gado- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Bahari ya shaida cewa Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya shirya wa barin kujerar sa ta gwamna duba da irin ayyukan…

Shugaban Najeriya Muhammadu Bahari ya shaida cewa Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya shirya wa barin kujerar sa ta gwamna duba da irin ayyukan da ya yi a jihar.

“Ganin irin wannan manyan ayyuka da Gwman Amusu ya yi, da sunayen da ya sanya wa aikin zaka tabatar ya shirya barin aikin cikin salama”

Shugaba Buhari ya shaida haka ne a ziyarar bude ayyukan da ya yi a Abeokuta a ranar Asabar din da ta gabata inda ya bude manyan ayyukan da suka hadar da katafaren ginin shari’a na jihar da ke Kobape da dakin kalon wasa wato tiyata mai daukar mutum dubu 10 da ke Okelewo, sai katafaren zauren zamani na sayar da kamfala ta adire da gidan talbijin din jihar na zamani da ke kan hanyar Ajebo.

A lokacin ziyararsa ya sami tarbar gwamnan jihar mai barin gado Sanata Ibikunle Amusu da na Legas na Legas Akinwumi Ambode wanda shima ke dab da barin gado sai gwamnan Ondo Oluwarotimi Odunayo.