✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Badaru ya nada manya sakatarori 12

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da nadin manyan sakatarorin jihar 12 wadanda aka tura ma’aikatu daban-daban. Wadanda aka nada sun hada…

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da nadin manyan sakatarorin jihar 12 wadanda aka tura ma’aikatu daban-daban.

Wadanda aka nada sun hada da Alhaji Adamu Muhammad Dallah da Alhaji Maigari Usman Muhammad da Alhaji Alhassan Ibrahim Marke da Alhaji Tijjani Usman da Alhaji Muhammad B. Muhammad da kuma Dokta  Salisu Mu’azu.

Sauran su ne Alhaji Lawan D.  Baba da Alhaji Ado Maigari Sadik   da Alhaji Muhammad Bello Dutse da Injiniya Gambo S. Malam da Alhaji Umar Sule Gwaram    da kuma Alhaji Lawan Ahmed Aliyu

A yayin da yake jawabi wajen  rantsar da manyan sakatarorin wadda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya hore su kan su rike amanar da Allah Ya dora musu kuma su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamna Badaru ya ce ya amince da ba su mukamann ne saboda kwazonsu da kulawarsu a kan aiki da kuma kokarin kwtanta gaskiya da suka nuna a baya.

Gwamna Badaru ya ci gaba da cewa “Duk da haka muna bukatar ku ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen ciyar da jihar nan gaba ta fuskar da ta dace”

Daga nan sai ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yi wa jama’a ayyukan more rayuwa da nufin bunkasa tattalin arzikin jihar.