Da Dumi Dumi

Gwamna Badaru ya nada mataimaka ga matansa 3

Gwamna Muhammadu Badaru na Jihar Jigawa
Gwamna Muhammadu Badaru na Jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya nada mataimaka na musamman ga matansa uku. A cikin mataimaka 51 da Gwamnan ya nada akwai masu taimaka masa na musamman akan fitilun hanya da kuma mai lura da adadin jama’a.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, a cikin jadawalin sunayen mataimakan akwai Sa’adatu Bashir Muhammed, mataimakiya ta musamman ga matar Gwamnan ta farko, sannan Mariya Muhammed Muktar mataimakiya ga matar Gwamna ta biyu sai kuma Aisha Garba, Mataimakiya ga matar Gwamnan ta uku.

An bayyana Jadawalin sunayen Mataimakan Gwamnan tare da ayyukan da zasu aiwatar, sai dai kawai na matan Gwamnan ne ba a sanar da ayyukan su ba.

 

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya