✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna bai isa ya rusa shugabannin kananan hukumomin Oyo ba – Kungiyar ALGON

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON) reshen Jihar Oyo, ta ce, ba ta yarda da umarnin rusa shugabannin kananan hukumomi 33 da yankunan raya…

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON) reshen Jihar Oyo, ta ce, ba ta yarda da umarnin rusa shugabannin kananan hukumomi 33 da yankunan raya kasa 35 (LCDA) a Jihar Oyo da sabon Gwamnan Jihar Injiniya Seyi Makinde ya bayar a ranar 29 ga Mayu ba lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki.

Kungiyar ta ce, ba za ta sabu ba kuma za su ci gaba da yin aiki a ofisoshinsu domin zabarsu aka yi ba nada su aka yi ba.

Gwamna Seyi Makinde ya lashe zaben Gwamnan Jihar Oyo ne a karkashin Jam’iyyar PDP, kuma Babban Jojin Jihar Oyo, Mai shari’a Munta Abimbola ne ya rantsar da shi da Mataimakinsa Alhaji Rauf Olaniyan a gaban dimbin jama’a a filin wasa na Obafemi Awolowo da ke Ibadan.                                                                                                                                             A jawabinsa na farko ga al’ummar jihar bayan rantsuwar, Gwamna Seyi Makinde ya bayar da umarnin soke biyan kudin makarantar firamare da sakandare da tsohuwar gwamnatin APC, ta bullo da shi na  Naira dubu uku ga kowa ne dalibin sakandare a zangon karatu na 1 a jihar.

Haka Gwamnan ya bayar da umarnin rusa dukkan shugabannin hukumomi da kamfanonin gwamnati da shugabannin kananan hukumomi 33 dana yankunan raya kasa (LCDA) 35. Ya umarci kowane shugaba ya hanzarta mika ragamar mulkin hukumarsa ga sakatare ko babban jami’in da ke aiki a karkashinsa.

Umarnin rusa shugabannin kananan hukumomin yana kunshe ne cikin sanarwar da sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati Mista Bisi Ilaka ya karanta a Gidan Rediyo da Talabijin na Jihar (BCOS.

Sanarwar ta bayar da umarnin rufe asusun ajiyar bankunan wadannan hukumominan take.

Kuma Gwamna Makinde ya bayar da umarnin dakatar da aikin manyan sakatarori 11 da tsohon Gwamna Abiola Ajimobi ya nada tare da rantsar da su mako 2 kafin ya mika mulki.

Sabuwar Gwamnati ta umarci  manyan sakatarori da kowanne ya koma ga mukamin da yake rike da shi a baya har zuwa lokacin da kwamitin da aka nada zai kammala binciken kan hanyar da aka bi wajen nada su bisa mukaman manyan sakatarori a cikin kurarren lokacin mika mulkin.

Nade-naden manya da kananan mukaman gwamnati da tsohon Gwamna Abiola Ajimobi ya yi mako 2 kafin ya bar gado ya sha suka daga jama’a tun a lokacin inda suke nuna cewa, an yi haka ne domin barin baya da kura da cusa gabar siyasa a tsakanin al’ummar jihar.

Cikin jawabinsa a ranar da aka rantsar da shi Gwamna Seyi Makinde ya ce gwamnatinsa za ta yi watsi da siyasa domin gudanar da aikin ci gaban miliyoyin al’ummar jihar da suka yi amfani da kuri’unsu wajen zabarsa a matsayin Gwamna.