✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna El-Rufai ya ba ilimi kashi 25 na kasafin kudin badi

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya mika wa Majalisar Jihar kasafin kudin badi na Naira biliyan 257 da miliyan 900 inda ya ce gwamnatinsa…

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya mika wa Majalisar Jihar kasafin kudin badi na Naira biliyan 257 da miliyan 900 inda ya ce gwamnatinsa na shirin kashe Naira biliyan 64 da miliyan 640  wato kashi 25.07 na kasafin kudin a bangaren ilimi.

Gwamnan wanda Mataimakiyarsa Dokta  Hadiza Balarabe ta wakilta wajen mika kasafin kudin, ya ce kasafin na badi, an yi masa taken sanya bukatun mutane a gaba, wanda kuma hakan ya yi daidai da taken gwamnatinsa.

Ya ce a cikin kasafin karatun firamare da sakandare zai zama wajibi ga kowane yaro dan Jihar Kaduna kuma kyauta, kuma gwamnatin za ta tabbatar da an yi amfani da wannan tsari ko shiri na gwamnati domin ganin kowani yaro ya samu ilimi a jihar.

“Mai girma Shugaban Majalisa, wannan kasafin kudin na badi ya kai Naira biliyan 257.9. Kasafin da aka ware wa sashen ilimi shi ne Naira biliyan 64.64 wato kashi 25.07, sashen lafiya kuma Naira biliyan 39.61 wato kashi 15.36 sai ayyuka Naira biliyan 66.34 wato kashi 25.72 na kasafin. Wannan ya nuna cewa za mu mayar da hankali ne kan ci gaban mutane da kuma gudanar da ayyuka,” inji Gwamnan

Ya ce gwamnatinsa ta bayyana niyyarta ta fadadawa tare da bada dama ga ilimi wanda hakan ya sa aka fito da tsarin bada ilimi kyauta kuma dole har sai an kammala sakandare ko makarantar koyon sana’o’i.

A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali ya yaba wa gwamnatin ne bisa kasancewarta ta farko wajen fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikatan jihar.

Sannan ya nanata aniyar ’yan majalisar na bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin a ciyar da jihar gaba.