✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Fashola ya sanya hannu a kan dokar kone gawa

Gwamna Babatunde Raji Fashola na Jihar Legas ya sanya hannu a kan dokar nan da ake cece-kuce a kan ta, wacce ta ba jama’ar jihar…

Gwamna Babatunde Raji Fashola na Jihar Legas ya sanya hannu a kan dokar nan da ake cece-kuce a kan ta, wacce ta ba jama’ar jihar damar kone gawarwakin ’yan uwansu idan suna bukata.
Gwamnan ya sanya hannu a dokar ce bayan da majalisar dokokin jihar ta shafe watanni tana muhawara a kan ta, saboda sukar da wadanda ke adawa da dokar suka yi ta yi, inda suka bayyana cewa ta saba wa al’ada da addinin mutanen jihar.
Yayin da yake jawabi jim kadan bayan ya sanya wa dokar hannu, Gwamnan ya ce dokar ba dole ba ce a kan kowa, kuma sanya mata hannu da ya yi ya nuna yadda mutane ke kara wayewa a jihar, sannan ya yaba wa kokarin da ’yan majalisar suka yi na zartar da ita.
Ya ce matakin da ’yan majalisar suka dauka ya nuna cewa kone gawa shi ne abin da ya fi dacewa.
Kwamishinan shari’a na jihar kuma atone-janar, Mista Ade Ipaye ya ce dokar ta ba da zabi dangane da kone gawa. “Dokar ba dole ba ce, ta ba da zabi, mutum ne zai bayyana yana so a kone gawarsa idan ya mutu ko kuma daya daga cikin danginsa da ya kai shekara 18”. Inji shi.