✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Geidam ya kaddamar da motocin tallafin man fetur na SURE-P

Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya kaddamar da motoci kirar Toyota Bus masu daukar mutane 16 guda 50, wadanda aka kiyasta kudinsu  kan Naira…

Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya kaddamar da motoci kirar Toyota Bus masu daukar mutane 16 guda 50, wadanda aka kiyasta kudinsu  kan Naira Miliyan 450. Motocin na karkashin shirin rarar man fetur na SURE-P, inda aka shirya bayar da rancen su ga wassu al’ummar jahar tare da rangwamen kashi 50 cikin 100 ga kowannensu.
 Gwamnan ya kaddamar da bashin motocin ne, a farfajiyar gidan gwamnatin jahar da ke garin Damaturu, yadda ya ci gaba da cewar, wadannan motoci an samar da su ne don tallafa wa al’umma ta wajen samun saukin harkokin su na tafiye –tafiye, ba tare da matsi ba a yayin da su kuma al’ummomin da za su amfana da wannan rance za su amfana matuka gaya, wajen habaka tattalin arzikinsu.
 Gwamnan ya ce wadannan motoci 50 an sayi kowacce kan  kudi Naira Miliyan takwas da rabi, kuma gwamnatin za ta bada su ne akan Naira Miliyan 4 da dubu dari 250, watau kowanne mutum da aka ba shi motar an masa rangwamen kashi 50 cikin 100.
 Ya kara da cewar, duk wanda ya amfana da wannan shiri na bada rancen motar zai biya ne a cikin wa’adin watanni 30.
 “Wannan rancen motoci tare da rangwame ya zo ne a bisa ga shirin nan na gwamnatin tarayya na rarar man fetur, don samar wa al’umma sauki a harkokin sufuri da kuma rage musu radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar bara,” a cewarsa.
 Ya hori wadanda suka samu wannan tallafi da su tabbatar da sun rage farashin kudin hawa mota, ta yadda zai bambanta da na sauran ‘yan kasuwa, kasancewar da ma an yi hakan ne don al’umma su amfana da kudaden rarar man fetur da ake samu.
 Alhaji Ibrahim Gaidam ya kuma umarci ma’aikatar matasa da walwalar jama’a da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri da makamashi da ke jahar, da su kula da yadda za’a tafiyar da wadannan motoci tare da  neman wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi da su cika dukkan sharuddan da aka gindaya mu su kafin a ba su motoci, Ya umarci ma’aikatun da su tabbatar da sahihancin direbobin da za su tuka wadannan motoci don kauce wa fada wa hannun batagari.
Shi kuwa shugaban kungiyar direbobi ta kasa (NURTW), reshen Jihar Yobe Alhaji Husaini Ibrahim a madadin kungiyarsu, ya mika godiyarsu ga gwamnan dangane da bada rancen wadannan motoci da ya yi ga al’umma.