✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Kwankwaso ya ziyarci kasuwar Mil 12 a Legas

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano ya ziyarci al’ummar Arewa da ke hada-hadar kasuwanci a kasuwar kayan abinci da ake yi wa lakabi da…

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano ya ziyarci al’ummar Arewa da ke hada-hadar kasuwanci a kasuwar kayan abinci da ake yi wa lakabi da kasuwar Mil 12 don sada dankon zumunci.
Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kai ziyara a makon da ya gabata, ya sami kyakkawar tarba daga shugabannin kasuwar da sauran dimbin al’ummar Arewa da ke sana’a a kasuwar, inda ’yan Kwankwasiyya suka sanya jar dara don nuna goyon baya da farin ciki da zuwan gwamnan.
Da yake jawabi, tsohon sakataren kasuwar kuma dan majalisar wakilai ta Jihar Kano mai wakiltar mazabar Rano, Honarabul Kabiru Alasan ya yaba wa gwamnan dangane da aikace-aikacen da yake gudanarwa a Jihar Kano.
Ya mika koken ’yan kasuwar dangane da kamen da wasu hukumomin Jihar Legas ke yi wa ’yan kasuwar.
Shi ma shugaban kasuwar Mil 12, Alhaji Haruna Muhammed ya yi godiya ga gwamnan dangane da ziyarar da ya kai musu.
Alhaji Haruna, wanda ya bayyana gwamnan a matsayin  jagoran ’yan Arewa, wanda yake kwato wa ’yan Arewa hakkinsu a kasa baki daya, ya jaddada goyon bayansa da jama’ar kasuwar Mil 12 ga Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.
“Babu shakka muna alfahari da kai. Mai girma gwamna, muna da matsaloli da yawa a kasuwar Mil 12, muna rokon gwamna zai taimaka mana don ganin an samu bunkasar tattalin arziki a kasuwar 12. Muna alfahari da kai, domin kai ne a yanzu kake kwato mana hakki. Saboda haka muna fatan Allah Ya sa ka zama shugaban Najeriya”. Inji shi.
Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi godiya dangane da goyon bayan da ’yan kasuwar suka ba shi, kuma ya bukaci ’yan Arewa da ke kasuwar su ci gaba da zama lafiya da sauran kabilun da ke hada-hada a kasuwar.
Ya yi alkawarin tattaunawa da shugabannin kasuwar da kuma gwamnatin jihar don ganin an yi maganin matsalolin da ke damun ’yan Arewa da ke hada-hada a kasuwar.