✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamna Lalong na yi wa al’ummar Hausa/Fulani adalci’

Garkuwan al’ummar Hausa/Fulanin yankin Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya ce Gwamnan Jihar Barista Simon Bako Lalong…

Garkuwan al’ummar Hausa/Fulanin yankin Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya ce Gwamnan Jihar Barista Simon Bako Lalong yana yi wa al’ummar Hausa/Fulani da ke jihar adalci, ta hanyar tafiya da su, a gwamnatinsa.

Alhaji Ya’u Bala Jingir ya bayyana haka ne,  lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a Jos, inda ya ce an dade ba a samu Gwamnan da yake tafiya da al’ummar Hausa/Fulani a Jihar Filato kamar Gwamna Lalong ba. Ya ce a da akwai abubuwa da dama da ba a yi da al’ummar Hausa/Fulani, a jihar.

Ya ce amma da zuwan Gwamna Lalong da kuma ganin yawan kuri’un da al’ummar Hausa/Fulani suka ba shi, ya tafi da su a gwamnatinsa.

“Tun a zuwansa na farko ya ba mu kwamishina. A yanzu kuma da ya sake dawowa ya sake ba mu kwamishina, kuma ya ba mu shugaban riko na Karamar Hukumar Jos ta Arewa. Wannan abu da Gwamna Lalong ya yi, ya tabbatar mana cewa yana da adalci,” inji shi.

Ya yi kira ga Gwamnan ya kammala ayyukan raya kasa da ya faro a unguwannin Hausawa na garin Jos, kamar yadda ya kammala aikin hanyar Unguwar Rogo da Unguwar Rimi.

Ya ce akwai wuraren da babu ruwan sha da asibitoci a unguwannin Hausawa da ke garin Jos. Don haka ya bukaci Gwamnan ya yi kokari ya samar da wadannan abubuwa a unguwannin.

Ya yi kira ga al’ummar Hausa/Fulanin jihar su ci gaba da zaman lafiya, domin dukkan abubuwan da suka samu a gwamnatin Lalong, sun same su ne, saboda zaman lafiyar da suke yi. Kuma su mara wa Gwamnan baya don samun nasarar gwamnatinsa.